34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Miji ya rushe gidan da ya ginama iyayen matar shi saboda ta rabu dashi

LabaraiLabaran DuniyaMiji ya rushe gidan da ya ginama iyayen matar shi saboda ta rabu dashi

Mijin ya rushe gidan matar dana mahaifiyar ta

Wani miji ya rushe gidan da ya ginama iyayen matar shi da kuma wanda ya gina mata sakamakon rabuwa da tayi da shi ta koma ta auri wani mutumin daban.

A ɗan gajeren bidiyon da ya karaɗe kafafen sadarwar zamani, an ga mutumin mai suna Francis Banda ɗan ƙasar Malawi tare da wasu mutane suna ta rushe gidan da ya gina ma matar shi da kuma wanda ya gina ma iyayenta biyo bayan rabuwa da tayi dashi taje ta auri wani mutumin.

Shekaru 13 suna tare da ita

Malawi 24 ta ruwaito mutumin ya na bayyana cewa shekarun su goma sha uku tare da matar a zaman aure. Ya kuma bayyana cewa ‘ya ‘ya uku suka haifa a wannan lokaci na auren nasu.

Ya ƙara da cewa, a lokacin da suke a tare, yayi ƙoƙarin gina ma matar tashi gida, haka nan ya yi ƙoƙarin gina ma mahaifiyar ta nata ita ma a can ƙauyen su.

Ya neme ta a waya bai sameta ba

Kamar yadda mijin ya bada bayani, matar tashi ta ƙulla alaƙa da wani mutum a asirce, inda bayan da alaƙar tasu tayi ƙarfi sai kawai ta rabu dashi ta koma wajen sabon masoyin nata.

Mijin matar, wato Francis Banda yace bayan barin ta gidan nashi yayi ta ƙoƙarin neman ta a waya amma daga ƙarshe sai yaji wani na miji ya ɗauka.

Wannan ne dai dalilin da ya fusata mijin wato Banda inda daga nan ne ya yanke shawarar zuwa ya rushe gidajen biyu, wato wanda ya gina ma matar da kuma wanda ya gina ma mahaifiyar ta ta.

Irin wannan matsala dai a yanzu ta fara zama ruwan dare a ƙasashen Afrika, saɓanin yadda aka santa a baya na cewar tafi faruwa a ƙasashen turai. A wasu lokutan, matsalar kan haifar da rikici kala-kala wanda a wasu lokutan ma kan iya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

A wani labarin na daban kuma, tsohon ministan tsaro a lokacin mulkin soji Theophilus Y Danjuma ya bayyana cewa sakacin gwamanti ne ya bawa ‘yan ta’adda dama suke yin abinda suka ga dama.

Ya bayyana hakan ne a wajen wani taron naɗin sarauta a garin Wukari, jihar Taraba. Inda ya ƙara da cewar ‘yan ta’addan so suke yi su ƙara yima Najeriya irin mulkin mallakan da aka yi a can baya.

TY Ɗanjuma wanda shima tsohon soja ne kuma masanin tsaro, ya taɓa zargin jami’an tsaro da haɗa kai da ‘yan ta’adda wajen kisan ‘yan Najeriya a shekarar 2018. Yace sun gaza wajen sauke nauyin dake kansu na kare ‘yan ƙasa daga hare-hare.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe