Sadiq Saleh, sabon mawaki wanda ya samu shahara bayan sakin wakarsa mai taken ‘Abin ya motsa’ ya bayyana burinsa a rayuwa inda yace yana son ko ina a duniya a san shi, kuma yanzu haka ya fara taka matakin.
A tattaunar da BBC Hausa tayi da matashin mai karancin shekaru, ya bayyana tarihinsa inda yace an haife shi a Maiduguri kuma ya taso sannan ya yi karatunsa a can.
Ya ce ya kwashe shekaru yana yin waka kasancewar tun yana karami yake da burin zama mawaki, daga nan kuma ya hadu da abokai masu irin ra’ayinsa.
A cewarsa, ya yi wakoki na siyasa da na aure daban-daban kuma bai samu shahara bane sai a wannan sabuwar wakar da yayi ta Abin ya motsa, wacce kowa ya san shi da ita.
Yayin da aka tambayeshi wakar da yafi so a duk wakokinsa, ya ce yafi son wakar Abin ya motsa, sai dai ba ita bace wakar da yafi shan wahala yayin rerata.
Ya ce wakar aure ta farko da yayi ne yafi wahala yayin yin ta. Ya shaida cewa ba ya da wani buri da ya zarce kowa na duniya ya san shi, kuma yanzu haka da alamu ya fara taka wannan mataki.
Babu farinciki a duniyar nan fiye da mace ta kasance matar aure, Matar Adam Zango
Safiya Chalawa, matar jarumin finafinan Kannywood, Adam A Zango ya bayyana ra’ayinta dangane da kasancewar mace matar aure a shafinta na Instagram.
A wallafar da tayi ranar Asabar, ta bayyana cewa abu ne mai matukar sanya mace murna ta kasance a cikin dakin mijinta kuma hakan yana kawo natsuwa mara misaltuwa.
Shi ma yana yawan yabonta tare da cewa diyarsa za ta yi alfahari nan gaba idan ta ganta a matsayin mahaifiyarta. A wannan sabuwar wallafa da tayi, cewa tayi:
“Yar uwata musulma mai aure, a duniyar nan babu abinda yafi kasancewarki mamatar aure dadi. Ki kasance mai yawan yi wa Ubangiji godiya, da ya azurta ki da miji na kwarai, ki kuma dinga nuna farinciki akan kokarinsa (mijinki).
“Ki yi masa godiya akan taya ki cikasa addininki da yayi, bayan aurenki da yayi.”
Ta ci gaba da shawartar mata akan yadda za su tafiyar da rayuwar aurensu ta hanyar kyautata wa mazajensu. Muna fatan Ubangiji ya ci gaba da zaunar da su lafiya tare da fatan samun zuri’a dayyiba.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com