24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Yadda matar aure ta shawarci mijinta yayi mata kishiyoyi bayan ta kasa samun haihuwa

LabaraiYadda matar aure ta shawarci mijinta yayi mata kishiyoyi bayan ta kasa samun haihuwa

Wata matar aure mai suna Nerimima Juma, ‘yar kasar Uganda wacce ta ba mijinta shawarar ya kara auro wasu matan ta zama abin magana a yanar gizo.

Nerimima ta bayyana cewa bata da wata matsala da yin kishi da wasu matan akan mijinta Asanasi Mulingomusindi.

A wani bidiyo da ta tashar Afrimax English ta saka a YouTube, matar auren ta kasa samun ciki tun bayan auren su da mijin na ta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Matar auren ta shawarci mijinta yayi mata kishiya

Domin magance matsalar, Nerimina ta shawarci mijinta ya karo aure domin samun wacce za ta haifa masa ‘ya’ya.

Asanasi ya dauki shawarar matar ta sa, inda ya kara auren wata matar wacce yanzu har ta haifa masa yara bakwai.

Abin ban sha’awar shine, bayan zuwan matar ta biyun, matar sa ta farko ita ma ta fara samun juna biyu wanda yanzu har ta haifi yara hudu.

Iyalan sun yi amanna cewa zuwan mace ta biyun ne ya bude hanyar su ta samun haihuwa.

Mutumin yanzu haka ya kara auren wata matar, inda yawan matansa ya zama guda uku yanzu.

Ga bidiyon nan kasa:

Budurwa tayi wuff da saurayin da ta fara turawa sako a Instagram

A wani labarin na daban Kuma wata kyakkyawar budurwa tayi wuff da saurayin da ta fara turawa sako a Instagram.

Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Tabellah, tayi wuff da kyakkyawan saurayin mijinta, shekara biyar bayan ta tura masa saƙo a shafin Instagram.

Tabeellah da mijinta sun yi aure a watan da ya wuce, shekara biyar bayan sun fara gaisawa a shafin Instgram.

Tabeellah taje kafar sadarwa ta Twitter inda ta bayyana labarin su ita da mijin na ta. Sannan ta kuma sanya hotunan shagalin bikin auren su. Ta dai saka hotunan ne a ranar Laraba 10 ga watan Agusta, 2022.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe