Wani lakcara da yaransa sun kai wa wata budurwa farmaki inda su ka yi mata tsirara tare da lakada mata dukan tsiya bayan ta samu hatsaniya da diyarsa, LIB ta ruwaito.
An dauki bidiyon Dr Fred Ekpe Ayokhai, lakcara a jami’ar tarayya ta Lafia da yaransa yayin da su ke mai wa budurwar mai suna Blessing Mathias hari a Jihar Nasarawa.
A daya daga cikin bidiyoyin, an ga Dr Fred rike da almakashi yayin da yake yankar rigar Blessing yayin da take rokonshi gafara.
Blessing ta rika rigarta da karfi da hannayenta don ta adana tsiraicinta amma yaran Dr Fred sun tilastata cire hannayenta don mahaifinsu ya yaga rigar ba tare da taba kirjinta ba.
Sannan sun nemi ta bai wa ‘yar uwarsu Emmanuella hakuri akan abinda ta yi mata a baya. Cikin biyayya Blessing ta durkusa tana ba ta hakuri, amma Emmanuella ta ki amincewa ta hakura.
Wannan yasa Fred ya ci gaba da yankar rigarta. Bayan yanke rigar har zuwa kwankwasonta, Blessing ta kwanta kasa don tsirara yayin da iyalan Dr Fred ke dukanta.
Wannan bidiyon ya dauki hankalin mutane da dama inda kowa ke kira ga hukuma akan daukar mummunan mataki akan Fred da yaransa.
Dama asali Blessing ce ta fara cin zarafin Emmanuella saboda namiji, an wallafa bidiyon Blessing yayin da take cin zarafinta. Duk da haka, mutane na ganin bai dace ba harin da ‘yan uwan Emmanuella su ka kai wa Blessing.
Yajin aikin ASUU: Lakcara ta koma tallar dankali saboda neman na tuwo
Wata lakcara a fannin sadarwa ta jami’ar Uyo, Christiana Chundung Pam ta fara tallar dankali don samun na tuwo, Legit.ng ta ruwaito.
An tattaro yadda lakcarar ta samu aikin koyarwar a shekarar da ta gabata kuma ta ce za ta ci gaba da siyar da dankalin har nan da shekara 5 in har hakan zai taimaka ilimin kasar nan ya gyaru.
Pam ta ce tana zuwa tallar kasuwar Akpan Andem da ke Uyo, a Jihar Akwa Ibom a matsayin hanyar rufawa kanta asiri.
Pam wacce ke sana’ar a kasuwa da cikin gari ta bayyana yadda ta koma gona don taya iyayenta noma yayin da take fatan za a koma daga yajin aikin babu dadewa.
Kamar yadda ta shaida:
“Na yanke shawarar komawa sana’ar siyar da dankali don samun na rufin asiri. Ban dade da fara koyarwa ba don ko shekarar ban yi ba, ban tara kudi ba kawai aka fara yajin aiki.
“Har fara rancen kudade nayi don in samu na cin abinci da biyan haraji. Sannan sai da na ranci kudade don biyan kudin haya don gudun ayi min korar kare.”
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com