Ada Joy Agwu Eme, ‘yar asalin Jihar Abia ce ta lashe gasar kyawun Najeriya. Ita ce mace ta 34 da ta lashe gasar kyawu a ranar Juma’a 21 ga watan Oktoban 2022 wanda aka aiwatar a Otal din Eko da ke Jihar Legas, LIB ta ruwaito.
Budurwar mai shekaru 24 da haihuwa ce ta zama zakakura inda ta zarce mata 36 da su ka shiga gasar inda ta zama sarauniyar kyawun Najeriya.
Miss Edo, Montana Onose Felix ce ta zama ta biyu inda aka nada ta a matsayin sarauniyar duniya ta Najeriya a shekarar 2022.
Miss Anambra, Genevieve Ukatu, Miss Abuja, Ifeoma Uzogheli da Miss Legas, Lydia Balogun su ne mutane na biyar da su ka tafi gida da mukamai, miss Supranational ta Najeriya, Miss Ecowas ta Najeriya da kuma Miss Tourism ta Najeriya dukansu.
Ada ce amshi kujerar Oluchi Madubuike wacce ta lashe gasar kyau ta Najeriya a shekarar 2021. Ga bidiyonta:
Kambun Sarauniyar Kyau ya riga ya hau kai na ‘yan bakin ciki sai dai su mutu – Shatu Garko
Shatu Garko mai shekaru 18 a duniya, ta ce duk da ta san cewa makiya za su cigaba da magana kan wannan nasara da ta samu, amma kambun sarautar Sarauniyar Kyau ya riga ya hau kanta kuma babu abinda za ta iya yi akan haka.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata jaridar Labarun Hausa ta kawo muku rahoton yadda Kwamandan hukumar Hisbah Harun Ibn-Sina, ya ce rundunar su ta Hisbah za ta gayyaci iyayen Shatu Garko domin amsa tambayoyi kan dalilin da ya sanya suka kyale ‘yarsu ta shiga gasar Sarauniyar Kyau.
Gasar ta Sarauniyar Kyau an gabatar da ita a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 2021 a dakin taro na Landmark Center, dake cikin Victoria Island, cikin jihar Lagos.
Garko wacce ta sanya Hijabi a lokacin gasar, ta lashe gasar, inda aka yi mata kyautar naira miliyan goma (N10m), da kuma bata damar zama a cikin gida na alfarma na tsawon shekara daya, da kuma sabuwar mota da sauran kyaututtuka na alfarma.
Sai dai kuma shugaban na hukumar Hisbah, ya ce abinda Shatu Garko ta yi ya sabawa addinin Musulunci, inda ya kara da cewa za su gayyaci iyayen budurwar saboda hakan ya zama izina ga ‘yan mata masu tasowa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com