Kyawawan hotunan kafin aure na wata budurwa ‘yar Najeriya da direban motar haya ta bolt sun karade shafukan sada zumunta.
Budurwar wacce zata zama amarya mai suna Omolayoeni ta dai shiga motar direban bolt din shekara biyu da suka gabata. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Budurwar ta ga direban ya birge ta sosai
A lokacin da suke tafiya, sai ta ga direban yana da kyau sosai, don haka sai ta tura masa Sako ta WhatsApp bayan nan, inda ta bukaci da ya ajiye lambar wayar ta.
Direban mai suna Akinsola ya yarda ya ajiye lambar wayar ta. Shekara biyu tun bayan haduwar su, soyayyar su tayi karfi har sun shirya yin aure yanzu.
An saka hoton yadda hirar su ta farko ta wakana a Twitter inda aka rubuta:
“To dai, shekara biyu da suka wuce, kanwata ta kira bolt inda ta ga kyakkyawan saurayi. Ta kasa jurewa dai har sai da ta tuntube shi.
Mutane sun tofa albarkacin bakin su
Olayemi Yemaji ya rubuta:
“Da ace direban bolt din ne yayi haka, da ance yayi cin zarafi. Amma tunda ba haka bane sai mu bi sahu a yi ta cewa Awwn.”
Olamilekan ya rubuta:
“Irin yanmatan da suka ki ba direbohin fuska suyi hira da su, za ka gan su anan suna cewa Awwn da ‘Ubangiji yaushe’ Walahi enigbadun.”
Justin Kaycee ya rubuta:
“Don Allah ta ya mutum zai yi rajista ya zama direban bolt ko Uber? Ina tunanin na bolt ya fi.”
lCyril Michael ya rubuta:
“Ina son irin wadannan matan, suna neman abinda suke so ko da ba suyi nasara ba, za su amince da hakan, ku sani cewa ba wata cutuwa a jaraba saa. Maza masu karamin tunani ne kawai za su ce ta kosa ne.”
Budurwa tayi wuff da saurayin da ta fara turawa saƙo a Instagram
Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Tabellah, tayi wuff da kyakkyawan saurayin mijinta, shekara biyar bayan ta tura masa saƙo a shafin Instagram.
Tabeellah da mijinta sun yi aure a watan da ya wuce, shekara biyar bayan sun fara gaisawa a shafin Instgram.
Tabeellah taje kafar sadarwa ta Twitter inda ta bayyana labarin su ita da mijin na ta. Sannan ta kuma sanya hotunan shagalin bikin auren su.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com