LabaraiGwamnati ce ta bar 'yan ta'adda suke abinda suka...

Gwamnati ce ta bar ‘yan ta’adda suke abinda suka ga dama – TY Danjuma

-

- Advertisment -spot_img

Tsohon ministan tsaro a lokacin mulkin soji Theophilus Yakubu Danjuma ya bayyana cewa sakaci gwamanti ne ya bawa ‘yan ta’adda dama suke yin abinda suka ga dama.

Mulkin mallaka ‘yan ta’addan ke son maimatawa

Ya bayyana hakan ne a wajen wani taron naɗin sarauta a garin Wukari, jihar Taraba. Inda ya ƙara da cewar ‘yan ta’addan so suke yi su ƙara yima Najeriya irin mulkin mallakan da aka yi a can baya, kamar yadda The Cable ta wallafa.

TY Ɗanjuma wanda shima tsohon soja ne kuma masanin tsaro, ya taɓa zargin jami’an tsaro da haɗa kai da ‘yan ta’adda wajen kisan ‘yan Najeriya a shekarar 2018. Yace sun gaza wajen sauke nauyin dake kansu na kare ‘yan ƙasa daga hare-hare.

Jami’an tsaro na haɗa kai da ‘yan ta’adda

“Jami’an soji na da wani abu a cikin ransu, suna haɗa kai da ‘yan ta’adda, suna kashe mutane, suna kashe ‘yan Najeriya. Suna taimaka ma shige da ficen ‘yan ta’adda, suna kuma basu mafaka. Idan kuna jiran sojoji su kare ku to ɗaya bayan ɗaya zakuyi ta mutuwa.” inji Ɗanjuma.

Sai dai a lokacin, rundunar sojojin Najeriya ta maida ma Danjuma martani mai zafi inda har kwamitin bincike suka sanya kan hakan. Inda suka bayyana cewa maganganun nashi ka iya ɓata sunan hukumar, tare da kawo hargitsi a cikin ƙasa.

Da ya ke cigaba da jawabi a ranar Asabar ɗin, TY Ɗanjuma ya ce yadda abubuwa ke tafiya a yanzu ya tabbatar da maganganun shi da yayi a baya.

“Wani lokaci a can baya da nayi ikirarin cewa jami’an tsaro ba sa so ko kuma basu shirya bamu kariya ba, don haka mu tashi mu kare kan mu, hukumar tsaro ce ta fara musanta iƙirarin nawa.

“Sun ce wai maganganuna duk ba gaskiya bane, sun shirya wani ɗan ƙaramin kwamitin bincike don bincika gaskiyar magana ta ko akasin haka.

“Sun gayyace akan naje na bada bayani amma naƙi zuwa. Sai suka rubuta cewa wai maganganuna duk shaci faɗi ne kuma duk bani da hujja. Amma yanzu kam hujjoji sun bayyana.

Ko wane yanki na fama da rashin zaman lafiya

“Yanzu ko ina a cikin ƙasar na fuskantar ta’addanci. Kuma abinda ake iya gani ne cewa ‘yan ta’addan nan waɗanda baƙin haure ne sai ɓata abubuwa suke yi kuma gwamnati ta kyale su suna ta shigowa cikin ƙasar.

“Suna ƙoƙarin ƙara yi mana mulkin mallaka sun mamaye ƙasar mu. Ƙasar da tafi kowacce ƙasa yawan baƙar fata, amma sai gashi wasu shashashun ‘yan ta’adda na neman durƙusar da ita.

“Addu’a itace, Allah da ya bamu ƙasar nan, shi zai bamu ƙwarin gwuiwar fuskantar maƙiyan mu, mu gano inda suke, mu zaƙulo su, kuma mu fatattake su daga ƙasar, inba haka ba kuwa to lallai Najeriya na tsaka mai wuya.” inji Danjuma.

A wani labarin mai alaƙa da wannan, kunji yadda wani mutum ya sanya gidaje shi kasuwa, ya siyar da motar shi domin fanso ‘ya ‘yan shi gurin masu garkuwa.

Wani mutum mai matsakaitan shekaru ya bayyana cewa ya sa gidajen shi a kasuwa, sannan ya siyar da motar shi sannan ya iya haɗa kuɗin karɓo ‘ya ‘yan shi daga hannun masu garkuwa da mutanen da suka ɗauki ‘ya ‘yan shi guda biyu.

Mutumin mai suna Lukman Aliyu, mai sana’ar kayan ƙarafa, wanda mazaunin garin Ilorin jihar Kwara ne, ya bayyana ma jaridar Punch cewa sai da ya sanya gidajen shi guda biyu a kasuwa, haka nan ya siyar da motar shi da kuma wasu kayayyaki kafin ya iya haɗa kuɗin da zai fanso ‘ya ‘yan shi.

Masu garkuwa da mutane sun ɗauke ‘ya ‘yan na shi Muhiddeen ɗan shekara 15 da kuma Abdulƙadir dan shekara 12 a ranar 13 ga watan Oktoban nan da muke ciki a gidansu dake Aseyori, yankin Alagbado dake ƙaramar hukumar Ilorin ta kudu dake jihar Kwara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama shi sannan a sakaya shi saboda ya lakada mata na...

Wata mata ta haihu a masallacin Annabi

Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma'aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu...

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne 'yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani...

An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka

Nabeela Syed, 'yar asalin ƙasar Indiya ta kasance mace musulma ta farko da aka zaɓa a matsayin 'yar majalissar...

Must read

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you