LabaraiNa sanya gidaje na kasuwa, na siyar da mota...

Na sanya gidaje na kasuwa, na siyar da mota ta don fanso yara na gurin masu garkuwa

-

- Advertisment -spot_img

Wani mutum mai matsakaitan shekaru ya bayyana cewa ya sa gidajen shi a kasuwa, sannan ya siyar da motar shi sannan ya iya haɗa kuɗin karɓo ‘ya ‘yan shi daga hannun masu garkuwa da mutanen da suka ɗauki ‘ya ‘yan shi guda biyu.

Mutumin mai suna Lukman Aliyu, mai sana’ar kayan ƙarafa, wanda mazaunin garin Ilorin jihar Kwara ne, ya bayyana ma jaridar Punch cewa sai da ya sanya gidajen shi guda biyu a kasuwa, haka nan ya siyar da motar shi da kuma wasu kayayyaki kafin ya iya haɗa kuɗin da zai fanso ‘ya ‘yan shi.

Masu garkuwa da mutane sun ɗauke ‘ya ‘yan na shi Muhiddeen ɗan shekara 15 da kuma Abdulƙadir dan shekara 12 a ranar 13 ga watan Oktoban nan da muke ciki a gidansu dake Aseyori, yankin Alagbado dake ƙaramar hukumar Ilorin ta kudu dake jihar Kwara.

Yadda masu garkuwa suka sace yaran

Lukman ya bayyana wa manema labarai cewa, da misalin ƙarfe sha biyu na dare (12am), lokacin suna ƙoƙarin zuwa su kwanta shida matar shi da ‘ya ‘yan shi su biyar, sai matar tashi tace taji alamar kamar wasu sun shigo cikin gidan.

Ya ƙara da cewar yana leƙawa sai ya hangi mutanen suna ta ƙoƙarin yanke ragar sauron ɗakin na sa. Ya ce shida matar tashi sunyi ƙoƙarin suyi ihu domin neman ɗauki daga makwabta amma sai barayin suka fara harbe harbe wanda hakan ya hana kowa fitowa.

“Nayi ƙoƙarin jifar masu garkuwar da kwalabe, amma duk da haka suka cigaba da yin harbi. Daga ƙarshe dai dana fahimci cewa babu makawa sai sun shigo, sai na umarci matata da ta shiga ɗaki ta kulle kanta da ‘yan ‘yan nata, nima na shiga na kulle kaina a banɗaki.

“Daga ƙarshe sunyi nasarar kutsa kai zuwa ɗakin matar tawa inda suka dake ta a ƙirji sannan kuma suka ɗauki yaran mu guda uku. A yayin da suke ƙoƙarin ficewa, wani ɗan sakai ya kai musu harbi inda suma suka mayar masa da harbi, amma harsashin bai yi mishi komai ba.

“A cikin hakan ɗaya daga cikin ɗaya daga cikin ‘ya ‘yan nawa ya samu ya kuɓuta, inda su kuma suka arce da yaran nawa guda biyu.”

Sun tafi da kuɗaɗe da wayoyi

Da aka tambaye shi ko sun ɗauki wani abu bayan nan, sai yace eh sun ɗauki wasu ‘yan kuɗaɗen sa sannan kuma sun tafi da jakkar matar tashi da wasu ‘yan kuɗaɗe, haka nan sun tafi da abin sha, da burodi da wayoyi, ciki harda ta wani mutum da ya kawo caji.

Yace da farko da suka kira sun buƙaci a basu naira miliyan ashirin ne, daga bisani kuma suka dawo miliyan goma. Bayan haka sun dawo zuwa miliyan takwas, inda daga ƙarshe aka daidaita a miliyan biyar.

Yace ya siyar da motar shi miliyan ɗaya da rabi, yan uwansa sun haɗa mishi dubu ɗari biyar. Sannan ya siyar da wasu kayayyaki amma duk da haka kuɗin basu haɗu ba. Ya sanya gidajen shi a kasuwa, amma da bai samu mai siye da sauri ba sai yayi amfani da gidajen wajen samun rancen cikon kuɗin da ya bayar aka sako mishi yaran nashi.

Sun buƙaci a kai musu giya da katin waya

Yace da aka gama haɗa kuɗin an bawa wani abokin shi wanda ya kai musu kuɗaɗen. Amma kafin nan sun buƙaci a haɗo musu da kwalebanin giya da kayan shaye-shaye da kuma katin waya. Bayan an kai musu kuɗaɗen sun ƙirga ne suka sako mishi ‘ya’yan nashi.

A wani labarin na daban kuma, wata matashiyar budurwa ‘yar shekara 23 ta bayyana yadda aikin ƙwaƙwalwa da aka yi mata ya sanya ta mance tunanin ta na yarinta, da sauran abubuwa, ciki kuwa har da iyayen ta.

Weronika Fafinska, mai kimanin shekara 23 tace tun a February 2014 lokacin tana da shekaru 14 ne dai likitoci suka gano cewa tana fama da ciwon kansar ƙwaƙwalwa.

Ta ce anyi mata aikin cire ciwon kansar da ya taru a cikin ƙwaƙwalwar tata a shekarar 2014 ɗin. Sai dai tace hakan sai da ya janyo ta mance abubuwa da dama, ciki kuwa har da iyayen ta dake jinyar tata a wannan lokaci.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama shi sannan a sakaya shi saboda ya lakada mata na...

Wata mata ta haihu a masallacin Annabi

Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma'aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu...

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne 'yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani...

An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka

Nabeela Syed, 'yar asalin ƙasar Indiya ta kasance mace musulma ta farko da aka zaɓa a matsayin 'yar majalissar...

Must read

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you