34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Yadda aikin ƙwaƙwalwa ya sanya budurwa mance iyaye da abokanan ta

LabaraiYadda aikin ƙwaƙwalwa ya sanya budurwa mance iyaye da abokanan ta

Wata matashiyar budurwa ‘yar shekara 23 ta bayyana yadda aikin ƙwaƙwalwa da aka yi mata ya sanya ta mance tunanin ta na yarinta, da sauran abubuwa, ciki kuwa har da iyayen ta.

Tun shekaru takwas baya take fama da ciwon kansa

Weronika Fafinska, mai kimanin shekara 23 tace tun a February 2014 lokacin tana da shekaru 14 ne dai likitoci suka gano cewa tana fama da ciwon kansar ƙwaƙwalwa.

Ta ce anyi mata aikin cire ciwon kansar da ya taru a cikin ƙwaƙwalwar tata a shekarar 2014 ɗin. Sai dai tace hakan sai da ya janyo ta mance abubuwa da dama, ciki kuwa har da iyayen ta dake jinyar tata a wannan lokaci, kamar yadda Dailymal ta wallafa.

Weronika wacce ‘yar asalin Edinburgh, Scotland ce, ta ƙara da cewa ko a lokacin da aka sanya ta a mota wajen komawa gida sai dai tayi rashin lafiya saboda a cikin ranta tana jin kamar bata taɓa hawa mota ba, gaba ɗaya bata san inda za’a je ba.

Ban iya gane komi ba bayan aikin ƙwaƙwalwar

Ta ƙara da cewar a lokacin da suka isa gida bata gane gidan ba, bata gane ɗakinta dama kayanta ba, bata gane komi ba.

“Ban ma san cewa runbun gashi yana iya daukar zafi ba, ban iya gane ko menene ƙwallo ba, duk da dai na iya gane wasu abubuwan kamar Jadawalin karatun lissafi na.”

Bata gane ‘yan makarantar su ba

Ta ƙara da cewar data koma makarantar su bayan aikin ƙwaƙwalwar bata iya gane ko mutum ɗaya ba cikin ɗaruruwan ‘yan makarantar tasu. Ko abokanenta na kusa ma bata iya ganewa ba.

A shekarar 2012 ne dai Weronika ta fara jin alamar ciwon wanda yayi sanadiyar kurumcewar kunnen ta na ɓarin dama. An yi mata hoton ƙwaƙwalwa wanda ya tabbatar da cewar tana da kansar ƙwaƙwalwa.

Tun bayan da aka yi mata aikin, ciwon kansar ƙwaƙwalwa tata bai ƙara motsawa ba har sai a shekarar 2021 da aka gwada aka ce mata ya ɗan ƙaru, amma ba sai anyi mata aiki ba.

A watan Agustan wannan shekara da muke ciki ma dai an auna anga cewa ciwon ya ɗan ƙara mamayar ƙwaƙwalwar tata. Ta ce rashin sanin yadda ciwon ke ta girmama yana ɗaga mata hankali.

A wani labarin na daban kuma, kunji cewa an kama wani Magidanci ya na ta lalata da ‘ya ‘yanshi mata bayan rabuwa da mahaifiyar su.

Wani magidanci dai yayi ta cigaba da yin lalata da ‘ya’yanshi ‘yan mata su biyu tun bayan rabuwa da yayi da mahaifiyar su wani lokaci can baya.

Kwamishiniyar walwala da jin ɗaɗin mata ta jihar Anambra tace an kama wani magidanci mai suna Nwobi, mai matsakaitan shekaru bisa tuhumar cewa yana lalata da ‘ya’yanshi mata su biyu; da mai shekara uku da kuma ‘yar shekara biyar.

Ma’aikatar walwala da jin ɗaɗin matan ce dai tare da haɗin gwuiwar jami’an tsaro na sibil difens suka yi nasarar cafke mutumin. Sun gudanar da samame ne kan mutumin a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoban nan da muke ciki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe