34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Gadon waƙa nayi, don babana makaɗi ne, Yawale Kwana Casa’in

LabaraiKannywoodGadon waƙa nayi, don babana makaɗi ne, Yawale Kwana Casa’in

Jarumin Kannywood, Auwal Ishaq, wanda aka fi saninsa da Yawale Dankurma a cikin shirin fim din Kwana Casa’in mai dogon zango ya bayyana cewa ya fi daukar kansa a matsayin mawaki duk da an fi saninsa a jarumi.

A tattaunawar da Mujallar Fim tayi da Auwal, ya bayyana cewa asali shi mawaki ne, sai dai ya fi shahara a fim kasancewar ya fara fitowa a finafinan Adam A Zango ne, daga bisani kuma ya fita a Kwana Casa’in.

Ya ce akan sanya sa a bangaren barkwanci ne kafin ya fito a matsayin Yawale Dankurma a Kwana Casa’in.

A cewarsa:

Amma gaskiya duk da na yi suna a shirin Kwana Casa’in, na fi daukar kaina a matsayin mawaki a halin yanzu. Saboda duk abinda na sanya a raina zan yi, sai Allah ya taimake ni na yi nasara. Hakan yasa ko da na fara fim ba ji a jikina cewa ba zan iya ba.

Ita kuma harkar waka, zan iya cewa na gara ne kasancewar mahaifina makadi ne. Don haka a wurinsa na gada.”

Yayin da aka tambaye shi dangane da daukakar da ya samu, cewa yayi:

A harkar fim na fi daukaka musamman a shirin Kwana Casa’in. Duk inda naje sai in ji ana kirana da Yawale Dankurma ko kuma saurayin Rayya.

Sanadin fim na je kasashe kamar Ghana, Nijar, Chadi, Kamaru da sauran manyan garuruwa a cikin kasar nan. Kuma muna fatan wannan daukakar da mu ka samu ta kai mu ga gamawa lafiya.”

Bidiyon Malam Ali na Kwana Casa’in yana kutuntuma wa Rayya ashar a wurin daukar fim

Wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani ya bayyana Sahir Abdul, wanda aka fi sani da Malam Ali a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango yana kutuntuma wa Rayya, abokiyar sana’arsa ashar na cin mutunci, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Alamu na nuna cewa a wurin daukar fim din aka yi wannan rikicin don daga bidiyon za ka gane cewa a gidan Bawa Mai Kada aka dauki bidiyonsa yana zagin.

A cikin bidiyon an ji inda Malam Alin yake korafi yana cewa ya zo wurin daukar fim ba shi da lafiya amma babu wani cikinsu da ya tambaye shi ya jikinshi kuma ana cewa an kula da shi.

An ji yana auna zagi sosai har yake cewa idan an ga dama a cire shi daga aikin.

Bayan wannan bidiyon, an ji inda Malam Alin ya kara tura wa Rayya zagi kwando-kwando yana kiranta da jahila inda itama ta mayar masa da martani da zage-zage masu zafi ta WhatsApp.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe