24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Ina neman afuwar tarin mazajen da na kasa a wurin nema auren amaryata, Sheikh Daurawa

LabaraiIna neman afuwar tarin mazajen da na kasa a wurin nema auren amaryata, Sheikh Daurawa

Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bai wa mazajen da su ka yi gasar auren matarsa, Haula’u hakuri bayan ya kasa su.

A wani sabon bidiyo wanda Freedom Radio da ke Kano ta saki a YouTube, malamin ya bayyana cike da farinciki yana bayar da hakurin.

Ga dukkan alamu an dauki bidiyon ne bayan an daura aurensa da zukekiyar amaryarsa, a cikin masallacin ne ya amshi abin magana inda ya ke bayar da hakurin.

A cewarsa, gasa ce aka shiga ta aure, kuma kowa ya san malami zai hada da addu’o’i idan zai shiga ko wacce gasa, watakil hakan ne yasa ya samu nasara.

Bidiyon wanda gajere ne ya tabbatar da rahoton da Labarun Hausa ta saki a kwanaki kadan da su ka gabata, wanda aka bayyana yadda malam yaje a matsayin Late Comer yayi wuff da zukekiyar budurwar.

Malama Haula’u asalin ‘yar jihar Kano ce, kuma mahaddaciyar Al’Qur’ani ce don ta lashe mukabakar Al’Qur’anin da aka yi na wannan shekarar.

Duk da dai mace ce mai karancin shekaru, majiyoyi sun bayyana cewa tana karatu a jami’ar Bayero da ke Kano.

Mace irin wannan tana da wahalar samu musamman idan aka kalli yadda take da kyau, ilimin addini da na boko ga kuma natsuwa wacce haddar da ke kanta ta samar mata.

Muna yi musu fatan alkhairi tare da yi musu addu’ar samun zuri’a dayyiba. Ga bidiyon malamin:

Waɗanda suka ɗora hoton amaryata su goge shi in ba haka ba – Sheikh Daurawa

Fitaccen malamin addinin Muslunci Sheikh Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya buƙaci waɗanda suka ɗora hoton amarya shi ana mata kwalliya a soshiyal midiya da suyi maza su goge shi.

Kwalliya ake mata a ɗakin mahaifiyar ta

Malam Daurawa, a hirar shi da gidan Radiyon Freedom yace kwalliya ake yi mata a cikin ɗakin mahaifiyar ta, amma aka samu wasu a ciki da suka ɗauke ta hotuna sannan kuma suka yaɗa su a soshiyal midiya.

“Amma wasu daga cikin waɗanda ba’a san ko su waye ba sun shiga har ɗakin babar ta sun ɗauki hoton ta ana yi mata kwalliya, kuma suka zo suna yaɗawa.”

Yaɗa irin hotunan fasadi ne

Ya cigaba da cewa yaɗa irin wannan ba abu bane da ya dace, musamman duba da cewa ita matar ba waje ta fito taje ta yi party ba ko wani abu makamancin haka, a cikin dakin mahaifiyarta aka ɗauki hoton.

“To kaga irin wannan duk wanda ya yaɗa ya yaɗa fasadi, yaci amana tunda ba biki akai ba, ba taro akai ba, ba wani guri aka je akai party ba, amma a ɗauko hoton mutum ana yaɗawa.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe