34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Magidanci na ta lalata da ‘ya ‘yanshi mata bayan rabuwa da mahaifiyar su

LabaraiMagidanci na ta lalata da 'ya 'yanshi mata bayan rabuwa da mahaifiyar su

Wani magidanci dai yayi ta cigaba da yin lalata da ‘ya’yanshi ‘yan mata su biyu tun bayan rabuwa da yayi da mahaifiyar su wani lokaci can baya.

Yara ne ‘yan mata su biyu

Kwamishiniyar walwala da jin ɗaɗin mata ta jihar Anambra tace an kama wani magidanci mai suna Nwobi, mai matsakaitan shekaru bisa tuhumar cewa yana lalata da ‘ya’yanshi mata su biyu; da mai shekara uku da kuma ‘yar shekara biyar.

Ma’aikatar walwala da jin ɗaɗin matan ce dai tare da haɗin gwuiwar jami’an tsaro na sibil difens suka yi nasarar cafke mutumin. Sun gudanar da samame ne kan mutumin a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoban nan da muke ciki.

Ance mutumin dai sun rabu da matar tashi tun wani lokaci a shekarar 2020, kamar yadda dai majiyar mu ta Punch ta ruwaito.

Likita ne ya tabbatar da anyi lalata da su

Kwamishiniyar walwala da jin ɗaɗin matan ta jihar Anambra Ify Obinabo, ta hannun mai taimaka mata kan harkokin watsa labarai Chidinma Ikeanyionwu, tace za’a hukunta wanda ake tuhuma nan bada jimawa ba.

Ta bayyana cewa bayan kuɓutar da yaran, an kaisu asibiti domin a duba lafiyar su, inda anan ne likitan dake kan aiki ya tabbatar musu da cewa lallai an taɓa yin lalata da ‘yan matan. Ta ƙara da cewa a lokacin da aka kaisu asibitin an samu raunuka a gaban su.

Da aka ji ta bakin yaran, sun tabbatar da cewa mahaifin nasu yana lalata da su, kuma su basu sha’awar ƙara komawa gidan nashi domin gudun abinda ka iya zuwa ya dawo.

Wanda ake tuhuma ya musanta

Sai dai kuma wanda ake tuhuma ya musanta zargin, inda yace baya da masaniya akan cewa wani yana yin lalata da ‘ya ‘yanshi ballantana kuma ace shi karan kanshi. Yasha alwashin ɗaukar mummunan mataki akan wanda ya zo ya kawo ƙarar shi kan hakan.

A wani labarin kuma, kunji Yadda wata mata ta auri maza biyu ba tare da ɗayan su ya iya gano hakan ba.

Labarin wata mata mai suna Acheing dai da ta auri maza guda biyu ba tare da ɗayansu yasan da ɗaya ba ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani. Matar  kuma ta cigaba da rayuwar ta ba tare da sun gano da hakan ba.

Ɗaya daga cikin su bai iya ganowa cewa matar tana da wanin mijin daban bayan shi ba, har sai ranar da suka haɗu a kan hanya kamar yadda majiyar mu ta Legit ta wallafa.

Motar tace ta tona ta a yayin da ɗaya mijin ya ari motar da nufin ya ɗan je ya dawo. Fitar shi ke da wuya sai yayi kaciɓus da wani mai gadi wanda ya shaida mishi cewa lallai wannan motar da yake akai ta matar shi ce.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe