27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Dalibar JS3 ta haihu tana tsaka da rubuta jarabawar BECE, ta dawo ta kammala jarabawar

LabaraiDalibar JS3 ta haihu tana tsaka da rubuta jarabawar BECE, ta dawo ta kammala jarabawar

Wata daliba mai dauke da juna wacce ke rubuta jarabawar kammala karamar sakandire ‘Basic Education Certificate Examination’ (BECE) a kasar Ghana ta dawo ta cigaba da rubutun jarabawar bayan ta haifi ‘ya mace.

Nakuda ta same ta tana cikin rubuta jarabawar

Dalibar mai shekara 17 a duniya ta fara nakuda ne yayin da take rubuta jarabawar a cibiyar Kechibi M/A R/C ranar Talata, 18 ga watan Oktoban 2022.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa an garzaya da ita zuwa wani asibiti a Nkwanta ta Kudu a yankin Oti, amma an tura ta zuwa asibitin Nkwanta.

Yarinyar dai ta haifi ‘ya mace da misalin karfe 10 na dare a ranar Talata sannan ta dawo ta karasa rubuta jarabawar.

Ko da manema labarai suka ziyarci cibiyar da safiyar ranar Laraba, sun samu cewa yarinyar ta dawo ta cigaba da jarabawar.

Ta bayyana dalilin da ya sa ta dawo ta kammala jarabawar

Yarinyar ta bayyana cewa tana da cikakkiyar lafiyar da za ta iya rubuta sauran jarabawowin da suka rage, inda take cewa tana so ta samu nasara domin cigaba da karatun ta a babbar makarantar sakandire.

Likitoci na cigaba da kula da jaririyar a asibitin Nkwanta ta Kudu domin tabbatar da lafiyar ta.

Yadda malamin da na dauka matsayin uba yayi yunkurin yin lalata da ni -Daliba

A wani labarin na daban kuma, wata daliba ta bayyana yadda malamin da ta dauka matsayin uba yayi yunkurin yin lalata da ita.

Wata daliba ta bayyana yadda malaminta data dauka kamar uba yayi yunkurin yin lalata da ita. Lamarin dai ya auku da ita ne a shekararta ta farko da shiga jami’a.

Dalibar ta ce ita sabanin irin daliban nan ne marasa kokari wanda ke bayar da kansu don samun cin jarabawa ga malamai, kokarin ta ne yasa har malamin na su ya santa yayi kokarin yin lalata da ita.

Da farko malamin ya fara nuna mata kulawa akan karatunta inda ya rika bata shawarwari kan yadda zata kara mayar da hankali akan karatun nata, kafin daga bisani ya bayyana hakikanin abinda ke ran sa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe