27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Yadda wata mata ta auri maza biyu ba tare da sanin su ba

LabaraiYadda wata mata ta auri maza biyu ba tare da sanin su ba

Labarin wata mata mai suna Acheing dai da ta auri maza guda biyu ba tare da ɗayansu yasan da ɗaya ba ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani. Matar  kuma ta cigaba da rayuwar ta ba tare da sun gano da hakan ba.

Babu wanda ya iya ganowa a cikin su

Ɗaya daga cikin su bai iya ganowa cewa matar tana da wanin mijin daban bayan shi ba, har sai ranar da suka haɗu a kan hanya kamar yadda majiyar mu ta Legit ta wallafa.

Motar tace ta tona ta a yayin da ɗaya mijin ya ari motar da nufin ya ɗan je ya dawo. Fitar shi ke da wuya sai yayi kaciɓus da wani mai gadi wanda ya shaida mishi cewa lallai wannan motar da yake akai ta matar shi ce.

Shi da wani mai gadi matar take aure

Mai gadin ya fito da wayar sa inda ya nuna masa hotunan ta, wanda anan take ya tabbatar da cewa lallai matar tashi ce. Kuma daga nan ne ya gano cewa su biyu take aure ba shi kaɗai ba.

Matar ta riga da ta tsara yanda take haɗuwa da mazajen guda biyu; ɗaya a cikin ranakun aiki, a yayin da ɗayan kuma take haɗuwa dashi a ranakun ƙarshen mako. Matar tayi musu ƙarya ne ta yadda asirin nata bazai tonu ba a tunanin ta.

Mijin ya wallafa a shafin sa na tuwita

Mijin mai suna Mjengoke ne ya wallafa labarin a shafin shi na tuwita. Ya wallafa rubutun kamar haka:

“Kawai ka ɗan aro motar matarka zaka ɗan zagaya a cikin gari. Kawai daga fakawar ka sai kaga wani mutum yazo yana tambayar ka cewar me kake yi da motar matar shi?

“Ka faɗa mishi cewa motar ai ta matarka ce, amma sai kawai ya kaika ofishin sa inda ya nuna maka takardun motar. Alhalin ita matar a can baya ta faɗa maka cewa bashi taci a can wajan aikinsu ta sayi motar.

“Ka nemi ya nuna maka hoton matar tashi, sai ya nuna maka, kwatsam! hoton ɗaya ne da na matarka (wacce kuka haifi ‘ya ‘ya 2 tare da ita). Tayi mishi ƙaryar tana aiki a wani kamfani, a ƙarshen mako ne kawai suke haɗuwa.

“Alhalin kai kuma matar taka tayi maka ƙaryar cewa tana zuwa karatu ne na masta digiri ɗin ta a wata jami’a a wannan ƙarshen makon, har na tsawon shekara ɗaya.”

A wani labarin kuma, fitacciyar jarumar fim ɗin Kannywood Yahanasu Sani wacce ta daɗe ana damawa da ita a masana’antar fina-finan Hausa ta bayyana cewa ita bata ga laifin Safara’u ba don ta koma harkar waƙa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin hirar ta da sashen Hausa na BBC cikin shirin su na daga bakin mai ita. Tace ita bata ga laifin Safara’u ba don ta koma waƙa, tana mata fatan Allah ya bata nasara ya bata abinda take nema.

Tace mutane da dama suna ta tambayar ta akan me yasa ba zata yima Safara’u faɗa ba kan yanayin yadda take gudanar da lamurran ta musamman ma da ta shiga harkar waƙe-waƙen.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe