Wata ‘yar Najeriya ta wallafa hotunanta akan yadda ciki ya mayar da ita abar kwatance wanda hakan ya yi matukar bai wa mutane mamaki, Legit.ng ta ruwaito.
A bidiyon da ta wallafa yayin da take da juna biyu, an ganta ta koma wata iriya yayin da ta sauya gabadaya bayan ta haihu.
Nan da nan hotunan su ka yadu a kafar sada zumuntar zamani ta TikTok inda mutane su ka dinga tofa albarkacin bakunansu.
Mutane da dama sun yi matukar mamaki saboda yadda su ka ganta da kyau, inda wasu su ka dinga tambayar idan shin dagaske ne.
Kamar yadda ta yi rubutu yayin da ta wallafa bidiyon inda tace:
“Na yi tunanin kyau zan yi idan na samu ciki, amma sauyin da nayi ya yi yawa. Ina bukatar adalci.”
Tabbas halittarta ta sauya don ta koma kamar kurar tashe, abin dai ba a cewar komai sai wanda ya gani.
Magidanci ya shiga hannun ‘yan sanda bayan ya dirkawa diyar sa ‘yar shekara 13 ciki
Jami’an ‘yan sandan jihar Ogun, sun cafke wani magidanci mai shekara 39 a duniya, Mfon Jeremiah, bisa zargin dirkawa diyar sa mai shekara 13 a duniya ciki.
Jeremiah, wanda yake zaune a rukunin gidaje na FIRRO kusa da Adesan, Mowe, a karamar hukumar Obafemi-Owode, ta jihar Ogun, ya shiga hannun hukuma bayan matar sa ta kai karar sa wurin ‘yan sanda. Jaridar The Punch ta rahoto.
An tabbatar da cafke wanda ake zargin
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana batun kamun a cikin wata sanarwa ranar Juma’a. Oyeyemi yace an cafke wanda ake zargin ne bayan mahaifiyar yarinyar ta shigar da korafi a ofishin ‘yan sanda na Mowe.
Kakakin hukumar yace:
Mahaifiyar yarinyar tayi korafin cewa ta gano cewa diyarta na dauke da juna biyu, sannan da ta tambayi yarinyar sai tace mata mahaifinta ne ya sadu da ita. An kai yarinyar asibiti inda aka tabbatar da cewa tana dauke da cikin wata hudu.
Bayan ya karbi korafin, DPO na Mowe, SP Folake Afeniforo, ya tura jami’an sa cikin gaggawa zuwa gidan wanda ake zargi inda aka taso keyar sa. Bayan yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ya yiwa diyar ta sa ciki, amma yayi ikirarin cewa asiri aka masa lokacin da ya aikata.
Ya gayawa ‘yan sanda cewa ya rika mafarkin saduwa da matarsa wacce suka dade da rabuwa, kafin ya gano cewa ashe da diyar ta yake saduwa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com