24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Anya babu tsafi?: Hotunan yadda kwalliya ta sauya halittar wata mata, ta koma tamkar budurwa

LabaraiAnya babu tsafi?: Hotunan yadda kwalliya ta sauya halittar wata mata, ta koma tamkar budurwa

Wani bidiyo wanda yake yawo a kafafen sada zumuntar zamani ya bayyana yadda halittar wata mata ta sauya gabadaya bayan an yi mata kwalliya, Legit.ng ta ruwaito.

A bidiyon anga matar babu kwalliya yayin da ake shirin yi mata kwalliyar inda asalin halittarta ta nuna.

Daga bisani kuma sai gata halittarta gabadaya ta sauya bayan an yi mata kwalliya, wannan lamari ya bai wa mutane da dama mamaki.

Bidiyon wanda wata @krakshq ta wallafa, anga matar yayin da aka shafa mata wani farin mai a fuskarta.

Sai dai bidiyon ya sanya mutane da dama sun karyata mai kwalliyar, inda su ke ganin kamar ta sauya wata ne daban.

Wasu sun zargi ta yi amfani da filter wurin daukar hoton kasancewar har hasken fata sai da matar ta sauya.

Hotuna: Yadda kwararriyar mai kwalliya ya tayar da komadar tsohuwa, ta maida ta danya shakaf

Wasu hotuna da su ka bazu a kafafen sada zumuntar zamani sun dauki hankula bayan an ga tsohuwar da ta kai akalla shekaru 70 da doriya dauke da kwalliya mai daukar hankali, a shafin Makeup Artists da ke Facebook.

Da farko za ka yi tunanin yarinya ce mai kananun shekaru amma mai kwalliyar ta wallafa hotunanta kafin ta yi mata kwalliyar da kuma bayan ta yi mata.

Nan da nan mutane su ka yi caa su na mamakin kwarewar mai kwalliyar akan yadda ta mayar da tsohuwa yarinya danya shakaf.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe