34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ni banga laifin Safara’u ba don ta koma waƙa – Yahanasu Sani

LabaraiKannywoodNi banga laifin Safara'u ba don ta koma waƙa - Yahanasu Sani

Fitacciyar jarumar fim ɗin Kannywood Yahanasu Sani wacce ta daɗe ana damawa da ita a masana’antar fina-finan Hausa ta bayyana cewa ita bata ga laifin Safara’u ba don ta koma harkar waƙa.

Jarumar tayi ma Safara’u fatan alkhairi

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin hirar ta da sashen Hausa na BBC cikin shirin su na daga bakin mai ita. Tace ita bata ga laifin Safara’u ba don ta koma waƙa, tana mata fatan Allah ya bata nasara ya bata abinda take nema.

Tace mutane da dama suna ta tambayar ta akan me yasa ba zata yima Safara’u faɗa ba kan yanayin yadda take gudanar da lamurran ta musamman ma da ta shiga harkar waƙe-waƙen.

Taimako yayi wuya a yanzu

“Idan ka tsaya ka duba, ita harkar rayuwa, kowanne fa da system ɗin da ya ɗauko wanda zai masa, na farko kenan. Na biyu kuma duniya yanzu kasan ta zama wata iri, duniya fa ba taimako, sai hassada, sai makirci.

“Idan mutum ya shiga cikin wani abu, a misali, idan ya tashi wannan abun da yake yi yana ɗan taimaka mishi, idan aka ce babu wannan abun, zai iya shiga wani hali.

“To da mutum ya ɗauka ya shiga wani hali, Ni gaskiya Allah ya sani, ni banga laifin Safara’u ba don ta koma waƙarta, Allah ya bata nasara. Allah ya bata abinda take nema.” inji Yahanasu.

Sai dai kuma tayi kira ga jaruma Safara’u duba da yanda ake ta surutu dangane da yanayin dabi’unta akan da tayi ƙoƙari ta gyara yanayin yadda take shigar ta da kuma sauran abubuwa.

“Kawai kuma shiga ce da ake cewa tana shiga wacce bata dakyau, to Allah ya duba kuma ta gyara ita kuma ta daina yi, Allah ya bata nasara.”

Haka nan kuma jarumar ta baiwa sababbin jarumai mata da suka shigo masana’antar ta Kannywood akan su riƙe gaskiya da amana, su riƙe mutuncin su, sannan kuma su girmama na gaba dasu, idan suka yi hakan to Allah zai taimake su a lamurran su.

Yahanasu takai aƙalla shekaru 20 tana fim

Yahanasu Sani ta bayyana cewa ta fara harkar fim tun sama da shekaru ashirin da suka gabata, kuma ta shigo fim ne ta dalilin wata ƙawarta. Tace Ɗan Azumi Baba ne farkon wanda ya fara sanya ta a cikin fim.

A wani labarin kuma, Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa wato ASUU tace har yanzu tana nan a kan bakan ta na cewar ba zata yarda da tsarin IPPIS da gwamnatin Najeriya ta zo da shi ba wajen biyan lakcarori albashin su da sauran kuɗaɗe.

Mataimakin shugaban hukumar na ƙasa Chris Piwuna ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a lokacin da yake tattaunawa da jaridar premium times ta tuwita.

Ya kuma ƙara da cewa duk da ƙoƙarin da kakakin majalissar wakilai yayi wajen ganin an biya malaman jami’o’i kuɗaɗen su da aka riƙe, har yanzu dai babu wani malamin da aka biya ko sisi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe