Masu garkuwa da mutane wanda yawan su yakai mutum 10 sun farmaki wani masallaci a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Masu garkuwa da mutanen sun halaka mutum daya sannan suka sace wani dan kasuwa tare da dansa a yayin harin da suka kai a masallacin.
An bayyana lokacin da harin ya auku
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun farmaki masallacin ne wanda yake a kwanar Jalo cikin unguwar Saminaka a Jalingo lokacin Sallar Magriba.
Yaron dan kasuwar da aka dauke dai dalibi ne a wata makarantar sakandire ne dake a yankin.
An addabi mutanen yankin da hare-hare
A cikin ‘yan watannin da suka gabata dai masu garkuwa da mutane sun halaka mutane ciki har da dan sanda sannan sun sace sama da mutum 30 a yankin.
Masu garkuwa da mutanen wanda ke gudanar da ayyukan su daga tsaunikan dake kusa da rafin Lamurde a karamar hukumar Ardo_Kola, sun tilasta mutane da dama yin kaura daga yankin.
Har ya zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton, ba a samu jin ta bakin kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ba.
Bayan karbar N6m kudin fansa, masu garkuwa da mutane sun bani N2000 nayi kudin mota -Cewar matar da aka sace
A wani labarin na daban kuma, wata matar da aka yi garkuwa da ita ta bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka bata N2000 tayi kudin mota bayan karbar N6m kudin fansa.
Wata mai bayar da shaida, Hajiya Fatima Ibrahim, ta gayawa wata babbar Kotu a Zaria cewa wadanda suka yi garkuwa da ita sun bata N2000 a matsayin kudin mota bayan sun karbi N6m a matsayin kudin fansa.
‘Yan sanda na karar Dalhatu Shehu, Lawal Aliyu-Bullet, Nuhu Ismaila da Nura Usman da laifukan fashi da makami, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma garkuwa da mutane.
Hafsat brahim tana bayar da shaida ne a matsayin shaidar mai kara a zaman da kotun ta dawo don cigaba da sauraron karar a babbar kotu dake Dogarawa, Zaria.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com