Tsohuwar jarumar Kannywood Hajiya Zakiyya Ibrahim, ta bayyana cewa ‘yan fim mutane ne masu tarbiyya.
Zakiyya Ibrahim wacce tauraruwar ta haskaka sosai a baya a masana’antar Kannywood, ta yi kira ga jama’a da su daina kallon ‘yan fim a matsayin lalatattun mutane. Ta bayyana hakan ne a wata hira da Mujallar fim tayi da ita.
Ta shawarci abokan sana’ar ta ‘yan fim
Jarumar ta kuma janyo hankalin abokan sana’ar ta na masana’antar Kannywood da su kiyayi yin abinda zai janyo musu magana.
“Mu ‘yan fim mu na da tarbiyya,” inji ta
Jarumar ta koma sana’ar waka
Jarumar wacce yanzu ta rikide ta koma mawakiya ta kuma bayyana cewa tana samun alheri sosai tunda ta koma yin waka.
Ya zuwa yanzu dai ta yi wakokin siyasa masu yawa, inda ta fi samun kudi, ban da na yabon Manzon Allah (SAW) da na soyayya wadanda su ma ta yi su da dama.
“Kamar yadda na daɗe ina yin fim a matsayi na na jaruma, kuma haka na daɗe ina ɗaukar nauyin shirya fim. To ita ma waƙar haka na daɗe da ita.” Inji ta
Ta ci gaba da cewa:
“Tun a 2008 na fara waƙa lokacin da aka buɗe ‘Hikima’.”
“A gaskiya tun daga shekarar 2019 na fi mayar da hankali na a kan waƙoƙin siyasa, saboda su ne za ka yi a biya ka, tunda yanzu babu kasuwar sidi, to a haka na yi wa ‘yan siyasa masu yawa waka da gwamnoni da ‘yan majalisu.
“Kuma gaskiya ina samun alheri sosai.”
“Sannan kuma na bude shafi na a YouTube ina saka wakokin da na ke yi. Don haka ina samun cigaba sosai.”
Ga masu bata sunan ‘yan Kannywood: Duk wanda yace kule, za mu ce cas!, Tijjani Faraga
A wani labarin na daban kuma, jarumin Kannywood Malam Tijjani Faraga yayi gargadi mai kaushi kan masu bata sunan ‘yan fim.
Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Malam Tijjani Faraga ya ce akwai masu ilimi da dama a cikin masana’antarsu don haka ba za su sake yarda wani ya bata sunansu ba.
Ya bayyana hakan ne ta wani rubutu da yayi ya tura wa Mujallar Fim inda yace:
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com