Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa wato ASUU tace har yanzu tana nan a kan bakan ta na cewar ba zata yarda da tsarin IPPIS da gwamnatin Najeriya ta zo da shi ba wajen biyan lakcarori albashin su da sauran kuɗaɗe.
Mataimakin shugaban ASUU ya bada bayani
Mataimakin shugaban hukumar na ƙasa Chris Piwuna ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a lokacin da yake tattaunawa da jaridar premium times ta tuwita.
Ya kuma ƙara da cewa duk da ƙoƙarin da kakakin majalissar wakilai yayi wajen ganin an biya malaman jami’o’i kuɗaɗen su da aka riƙe, har yanzu dai babu wani malamin da aka biya ko sisi.
Alƙawuran da suke so a cika musu
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU dai ta shiga yajin aiki ne a watan Fabrairun wannan shekarar biyo bayan gazawar gwamnati wajen cika musu wasu alƙawura da aka ɗauka a baya.
Alƙawuran da ASUU take so a cika mata sun haɗa da wasu sauye-sauye a wajen biyan albashi da alawus ɗin malaman, ƙarin kuɗaɗe da ake tura ma jami’o’i, sai kuma sabon tsarin biyan ma’aikata mai suna UTAS da jami’o’i suka zo da shi saɓanin na IPPIS.
Sai dai ita gwamnati a nata ɓangaren tace yin amfani da hanyoyin biyan albashi sama da ɗaya zai janyo ƙarin kashe wasu kuɗaɗen waɗanda ba dole bane gwamanti ta iya kashewa.
A tattaunawar tashi da premium times, mataimakin shugaban hukumar ASUU Piwuna yace lallai matsayar da suka ɗauka kan IPPIS ba zata sauya ba.
“Ba zamu karɓi tsarin IPPIS ba duk ta yanda aka juya shi, ba zamu taɓa amfani da tsarin a makarantun mu ba.” inji shi.
Muna son jami’o’i su ci gashin kansu
“Samun ‘yancin cin gashin kan jami’o’i shine abinda ke gaban mu ba wai abubuwan dake cikin IPPIS ba. Daga ofishin shugaban ma’aikata na gwamnatin tarayya ake tafiyar da ayyukan jami’o’i da shuwagabannin su. Mu kuma burin mu shine su cire hannayen su daga hidindimun jami’o’i.”
Ya kuma ƙara da cewar ASUU zata cigaba da bibiyar matakai na shari’ah dangane da yajin aikin da kotu ta sanya suka janye. Zasu yi ƙoƙarin gamsar da kotu cewa su suna mutunta duk hukuncin da ta yanke.
A wani labarin kuma, kunji cewa jami’an tsaron Najeriya sun yi nasarar cafke wasu mutane su biyu dake yima waɗanda ba ‘yan Najeriya ba katin ɗan ƙasa a sansani ‘yan gudun hijira a jamhuriyar Nijar.
Haɗakar jami’an tsaron farin sojoji da na Imagireshin da kuma na hukumar ‘yan sanda ne dai suka yi nasarar waɗannan masu rijistar katin ɗan ƙasa na bogi a jamhuriyar Nijar kamar yadda Dailytrust ta wallafa.
Kamar yadda jami’an tsaro suka bada bayanan, an kama waɗanda ake tuhuma ne a sansanin ‘yan gudun hijira dake Gagamari a cikin jamhuriyar ta Nijar. An kama su ne da laifin yima waɗanda ba ‘yan Najeriya ba katin ɗan ƙasa, suna sanya su a cikin ma’adanar bayanan Najeriya.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com