27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

An kama masu rijistar katin ɗan ƙasar Najeriya a Nijar

LabaraiLabaran DuniyaAn kama masu rijistar katin ɗan ƙasar Najeriya a Nijar

Jami’an tsaron Najeriya sun yi nasarar cafke wasu mutane su biyu dake yima waɗanda ba ‘yan Najeriya ba katin ɗan ƙasa a sansani ‘yan gudun hijira a jamhuriyar Nijar.

rajistar katin ɗan ƙasa na bogi suke yi

Haɗakar jami’an tsaron farin sojoji da na Imagireshin da kuma na hukumar ‘yan sanda ne dai suka yi nasarar waɗannan masu rijistar katin ɗan ƙasa na bogi a jamhuriyar Nijar kamar yadda Dailytrust ta wallafa.

Kamar yadda jami’an tsaro suka bada bayanan, an kama waɗanda ake tuhuma ne a sansanin ‘yan gudun hijira dake Gagamari a cikin jamhuriyar ta Nijar. An kama su ne da laifin yima waɗanda ba ‘yan Najeriya ba katin ɗan ƙasa, suna sanya su a cikin ma’adanar bayanan Najeriya.

An samu kayayyaki a hannun su

Darekatan watsa labarai na hukumar tsaro ta ƙasa, Manjo janaral Musa Danmadami ne ya bayyana ma  yan jarida hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a hedkwatar hukumar dake Abuja a ranar Alhamis ɗin nan.

Danmadami ya bayyana cewa abubuwan da aka samo a hannun su sun haɗa da na’urar yin rajistar katin ɗan ƙasa, na’urar fitar da takarda, injin yima takardu leda, na’urar bin diddiƙi da kuma janareto guda ɗaya.

Ya bayyana cewa dai a ranar 13 ga watan Oktoban nan da muke ciki ne dai jami’an tsaron ‘yan sanda dana Imagireshin suka yi nasarar cafke mutanen a sansanin ‘yan gudun hijira na Gagamari dake jamhuriyar Nijar.

Zamu gano ko menene suke kitsawa

Da yake tsokaci gami da amsa tambayoyin ‘yan jarida, tsohon darekatan watsa labaran hukumar, janaral Benard Onyeuko ya bayyana cewa lallai zasu gano koma menene  waɗannan mutane biyu da aka kama suke kitsawa.

Ya ƙara da cewa wannan aikin da jami’an tsaro suka yi ba ƙaramar nasara bace tunda har a ƙasar waje suna iya yin aiki. Yace wannan abun a jinjina musu ne.

A wani labarin kuma, kunji yadda wata budurwa ta kitsa sace kanta don zuwa shaƙatawa wajen saurayin ta.

‘Yan sanda sun kama wata budurwa mai kimanin shekaru goma sha tara wacce ta kitsa sace kanta don kawai taje ta shaƙata tare da saurayin ta.

Matashiyar budurwar dai wacce take a Matero dake yankin Lusaka na ƙasar Zambia ta bar gida ne a ranar 16 ga watan Oktoban nan da muke ciki da misalin ƙarfe huɗu na yamma (04pm), da zummar cewa zata je coci amma daga ƙarshe ta wuce gidan saurayin ta, daga nan tayi ƙaryar cewa an sace ta.

Faruwar hakan keda wuya, sai kawun budurwar mai suna Brighton Mwamba ya yi maza ya sanar da ‘yan sandan yankin cewa an ɗauke ‘yar ɗan uwan shi mai kimanin shekaru 19 akan haryata ta zuwa coci a ranar 16 ga watan Oktoba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe