24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Ƴar ƙasar Rasha da kusa halaka kanta don kayatar da mabiyanta na Instagram da hotuna

LabaraiƳar ƙasar Rasha da kusa halaka kanta don kayatar da mabiyanta na Instagram da hotuna

Wata tauraruwa a kasar Dubai amma ƴar asalin ƙasar Rasha, Viki Odintcova mai shekaru 23 ta raɓa saman bene yayin da abokinta namiji ya riƙe hannunta yayin da take lilo a bene hawa na 1,004, Sahafin USA Today ne ya ruwaito.

Tauraruwar ‘yar kasar Rasha ta yanke shawarar daukar hoto wanda zai yi matukar daukar hankalin jama’a yayin da take lilo a babban bene na Dubai.

An dauki bidiyon nata ne sannan ta daura shi a Instagram yayin da wani namiji yake riƙe da hannun Viki Odintcova a benen.

Hoton ya dauki hankulan dubbannin jama’a a Instagram akan yadda ta kusa sadaukar da rayuwarta akanshi, mutane sun yi matukar mamaki.

Cayan Group, wadanda su ka kera ginin, sun caccaki wannan hoton na Odintcova wanda tayi shi ba tare da sanar da kamfanin ba ko kuma neman wata hanyar da zata kare kanta.

Yayin ake wasu shagulgula a benen Cayan, ana samun wasu kwararru da ke samar da hanyar kariya kamar yadda Gizel Daher, darektan kasuwanci da sadarwa ya bayyana a wata takarda da ya saki ranar Juma’a.

Babu yadda za ayi ace Ms. Odintcova ba ta da laifi, kuma muna nan mu na sanya matakan tsaro don gudun irin haka ya auku nan gaba,” a cewar Gizel Daher.

Kamfanin ta bayyana cewa za ta dauki matakin shari’a akan matar. Odintcova ta sanar da The National cewa bata da niyyar kara maimaita abinda tayi amma ta ce ya dace ace an biya ta da wadanda su ka yi mata hoton kudin diyya.

Ya kamata a biya mu kudin diyya saboda bayyana hatsarin ginin da muka yi,” a cewar Odintcova ga The National ta wani sako da ta tura ta yanar gizo.

Mun je saman ne ba don yin wani mummunan abu ba, da wani ya lallaba ya halaka kansa ko kuma ya aiwatar da wani ta’addanci.

Shugaban rundunar ‘yan sandan Dubai, Manjo Janar Khalil Ibrahim Al Mansouri ya sanar da The National cewa sun gayyaceta inda su ka sa ta sanya hannu akan cewa ba za ta sake makamancin hakan ba ta hanyar sa rayuwarta a hatsari.

Odintcova ta sanar da jaridar cewa tana mai bayar da hakuri kuma za ta sanya hannu akan takardar da ‘yan sanda su ka tura mata ta yanar gizo.

Yadda azaba ta komadar da sojan Ukraine bayan kwashe watanni 4 tsare a Rasha

Hoton wani sojan kasar Ukraine ya bayyana a shafukan sada zumuntar zamani wanda hakan ya girgiza zukatan jama’a da dama kamar yadda Instablog9ja ta ruwaito.

A wani hoto wanda mutane da dama jikinsu yayi sanyi an ga yadda ya karmashe ya lalace bayan kwashe watanni 4 a tsare.

Shafin Defense of Ukraine ne ya wallafa inda ya bayyana cewa:

“Sojan kasar Ukraine, Mykhailo Dianov yana cikin sojoji masu nasarar da su ka iya jurewa kuma da ransu yayin da Rasha ta kama su ta tsare. Wannan abin ban tausayi ne.”

Nan da nan mutane su ka dinga tsokaci iri-iri dangane da yadda halittarsa ta sauya. Wasu su na ganin bakar azaba da rashin cin abinci ne ya mayar da shi haka.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe