36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Yarinya ta sha kuka bayan mamarta ta shiga gasar rawa don samun injin niƙa ta faɗi

LabaraiYarinya ta sha kuka bayan mamarta ta shiga gasar rawa don samun injin niƙa ta faɗi

Wata ‘yar Najeriya ta dauki hankalin mutane da dama bayan an ganta a bidiyo tana rusa kuka saboda mahaifiyarta ta shiga gasar rawa don samun injin nika amma ta fadi, Legit.ng ta ruwaito.

Wata ma’abociya amfani da kafar TikTok mai suna @amazing_people111, ta wallafa wani bidiyo inda ta bayyana cewa mata goma sun shiga wata gasar rawa don su samu injin nika.

Lamarin ya tayar wa wata yarinya hankali inda ta dinga rusa kuka yayin da ta nemi mahaifiyarta. Matar wacce ake kyautata zaton mahaifiyarta ce ta dawo ta rarrasheta daga bisani inda itama daga baya aka ga ta fashe da kuma.

An ga matar tana goge hawayenta da zani wanda ya sauka daga idanunta. Kamar yadda wacce tayi wallafar tace a kasar bidiyon:

“Na tausaya mata, mahaifiyarta ta fadi gasar rawar da ta shiga wanda hakan ya hana ta samun injin nika. Cikin mutane goma da su ka shiga gasar rawar mutane biyu ne kadai su ka yi rawar dakyau. Kuma su ne za su wuce da injin nika gida.

Yaro mai aikin birkilanci yana kuka ya koma makaranta, bidiyon sa ya dauki hankula

Kamorudeen, karamin yaron nan wanda bidiyon sa yana aikin birkilanci yana kuka, ya karade yanar gizo ya koma makaranta.

Wannan labarin mai dadin saurare dai wani mai suna Lukman Samsudeen ya sanya shi a manhajar TikTok. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Labarin Kamorudeen ya bazu ne bayan bayyanar bidiyon sa yana kuka yana aikin birkilanci.

Bayyanar bidiyon sa ya sosa zukatan mutane da dama a yanar gizo

Bidiyon ya sosa zukatan mutane sosai inda aka rika tambayoyin ko ina iyayen sa suke da kuma meyasa yake aikin karfi yana dan karamin yaro da shi.

Nan da nan sai ta bayyana cewa mahaifin sa ya rasu sannan yana ganin mahaifiyar sa ne sau daya kawai a shekara a cikin watan Disamba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe