‘Yan sanda sun kama wata budurwa mai kimanin shekaru goma sha tara wacce ta kitsa sace kanta don kawai taje ta shaƙata tare da saurayin ta.
Matashiyar budurwar dai wacce take a Matero dake yankin Lusaka na ƙasar Zambia ta bar gida ne a ranar 16 ga watan Oktoban nan da muke ciki da misalin ƙarfe huɗu na yamma (04pm), da zummar cewa zata je coci amma daga ƙarshe ta wuce gidan saurayin ta, daga nan tayi ƙaryar cewa an sace ta.
Faruwar hakan keda wuya, sai kawun budurwar mai suna Brighton Mwamba ya yi maza ya sanar da ‘yan sandan yankin cewa an ɗauke ‘yar ɗan uwan shi mai kimanin shekaru 19 akan haryata ta zuwa coci a ranar 16 ga watan Oktoba kamar yadda nahiyar mu ta Face of Malawi ta wallafa.
Sai dai ance bayan hakan an yi mata wata allura data gusar mata da hankali, inda daga bisani aka ɗauke ta aka kaita wani gurin daban.
Bayan haka, wasu sun kirawo wani daban daga cikin kawunnan budurwar, inda suka shaida mishi cewa sun sace ta, kuma in ba’a kawo dubu hamsin (K50,000) na kuɗin ƙasar a cikin awanni 48 ba, to lallai wani mummunan abu zai iya faruwa da ita.
A ranar 17 ga Oktoba, wata daga cikin gwaggwannin budurwar ta kira wayar tata da misalin ƙarfe 12 na rana sai tai ɗauka sannan take faɗa mata cewa wai ita dai kawai ta tsinci kanta a wani ɗaki mara tagogi ita da wasu ‘yan mata aƙalla 10 da aka sato.
Daga nan ‘yan sanda sun tsananta bincike inda daga ƙarshe a ranar Laraba, 19 ga Oktoba, suka gano ta a gidan saurayin ta. Tuni ‘yan sanda suka iza ƙeyarta, inda zata fuskanci shari’a a gaban kotu.
A wani labarin na daban, fitaccen mawaƙin nan na masana’antar Kannywood Tijjani Gandu wanda kuma yayi fice a waƙoƙin siyasa dana yabon manzon Allah S.A.W ya bayyana cewa ‘yan ɗariƙar Kwankwasiyya kaɗai yake yima waƙa.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da mujallar Fim, inda ya bayyana cewa da waƙoƙin ‘yan kwankwasiyya yayi tashe musamman ma dai waƙar Abba gida gida wacce tayi fice a zaɓen 2019.
Ya ƙara da cewar shi dama kowa yasan cewa mawaƙin kwankwasiyya ne musamman ma dai a cikin Kano. A saboda da haka babu wani ɗan siyasa da zai yi ma waƙa face ɗan ɗarikar kwankwasiyya.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com