Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami wani babban jami’in gwamnatin sa daga mukamin sa.
Shugaba Buhari ya kori Effiong Akwa, shugaban hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) daga bakin aikin sa.
Darektan watsa labarai ta ministirin Neja Delta, Patricia Deworitshe, ta bayyana hakan inda ta kara da cewa shugaba Buhari, ya sanar da kafa sabbin tawagar masu gudanarwa da kwamitin jagoranta na hukumar ta NDDC. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Tuni har an tura sabbin sunayen sabbin jagororin hukumar ga majalisar dokoki
A cewar sanarwar, sunayen sabbin masu gudanarwa na hukumar za a mika su ga majalisar dokokin domin amincewa da su.
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da korar shugaban rikon kwarya na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), Mr Effiong Okon Akwa, daga mukamin sa nan take daga yau Laraba 20 ga watan Oktoba, 2022,” Inji sanarwar
“An nada Mr Effiong Okon Akwa a matsayin shugaban rikon kwarya na hukumar zuwa lokacin da za a kammala binciken kwakwaf kan ayyukan hukumar NDDC, wanda yanzu haka an kammala.”
“Shugaba Buhari ya kuma amince da kafa sabbin tawagar masu gudanarwa da shugabannin gudanarwa na hukumar NDDC bisa hurumin sashi na 5(2) na dokar kafa hukumar NDDC ta shekarar 2000. Za a mika sunayen sabbin mutanen da aka zabo ga majalisar dokoki domin amincewa da su.”
Aisha Buhari ta nemi afuwar ‘yan Najeriya kan matsalar tattalin arziki da ake fama da shi tun shekarar 2015
Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari a ranar Juma’a, 30 ga watan Satumba, ta nemi afuwar ‘yan Najeriya game da matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a fadin kasar tun bayan hawan mijinta kan karagar mulki.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Aisha ta nemi afuwar ne a lokacin da take jawabi a wajen taron sallar Juma’a na musamman da kuma lacca na musamman na ranar samun ‘yancin kai karo na 62.
Ta yi nuni da cewa duk da cewa gwamnati mai ci ta gaza amma akwai bukatar kowa da kowa ciki har da malaman gargajiya da na addini su hada kai don samar da ingantacciyar Najeriya. Dole ne dukkan ‘yan Najeriya su hada kai domin kawo karshen wahalhalun da ake ciki.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com