Fitaccen mawaƙin nan na masana’antar Kannywood Tijjani Gandu wanda kuma yayi fice a waƙoƙin siyasa dana yabon manzon Allah S.A.W ya bayyana cewa ‘yan ɗariƙar Kwankwasiyya kaɗai yake yima waƙa.
Da waƙar Abba Gida-gida nayi suna
Ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da mujallar Fim, inda ya bayyana cewa da waƙoƙin ‘yan kwankwasiyya yayi tashe musamman ma dai waƙar Abba gida gida wacce tayi fice a zaɓen 2019.
Ya ƙara da cewar shi dama kowa yasan cewa mawaƙin kwankwasiyya ne musamman ma dai a cikin Kano. A saboda da haka babu wani ɗan siyasa da zai yi ma waƙa face ɗan ɗarikar kwankwasiyya.
Ni mawaƙin kwankwasiyya ne kaɗai
“Kuma ni da man a siyasa ni mawaƙin Kwankwasiyya ne. In dai a Kano ne, babu wani ɗan siyasa da zan yi wa waƙa sai ɗan Kwankwasiyya da ‘yan cikin ta. Kamar yadda ka ji mu na cewa, ba mu fara don mu daina ba!”
Tijjani Gandu ya bayyana cewa bai taɓa tunanin cewa zai koma harkar waƙa ba. Ya bayyana cewa yayi sana’o’i da yawa ciki hada harkokin zane-zane wanda a cikin hakan ne ya ƙulla alaƙa da mawaƙa daga nan har ya fara harkokin waƙa.
Mawaƙin yace yakan je studio na mawaƙa daban-daban domin yayi musu zane wanda a hakan ne suka saba da mawaƙan wanda daga nan ne shima ya rikiɗe ya kama harkar waƙar.
“Da yake ina yin waƙoƙi na Mauludi a makarantar mu, sai ya zama na iya rubutun waƙoƙin yabon Manzon Allah da kuma na faɗakarwa. To sai na fara da na yabon Manzon Allah. Ina yi har aka fara sani na a cikin mawaƙa.” inji Tijjani Gandu.
Waƙoƙin da Tijjani Gandu yayi tashe da su
Tijjani Gandu dai yayi tashe sosai a ‘yan kwanakin baya. Waƙar ‘yar maye ce dai waƙar da aka fi sanin shi da ita, kamar dai yadda ya bayyana ma mujallar Fim. Waƙar Farin wata da waƙar Na Tuba na daga cikin waƙoƙin da aka san Tijjani Gandu da su.
Daga ƙarshe, mawaƙin yayi kira ga abokan sana’ar shi akan su riƙe mutuncin sana’ar tasu, su kuma kiyayi yin duk wani abu da zai zubar da mutuncin su da kuma mutuncin sana’ar tasu.
A wani labarin kuma, fitaccen malamin addinin Muslunci Sheikh Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya buƙaci waɗanda suka ɗora hoton amarya shi ana mata kwalliya a soshiyal midiya da suyi maza su goge shi.
Malam Daurawa yace kwalliya ake yi mata a cikin ɗakin mahaifiyar ta, amma aka samu wasu a ciki da suka ɗauke ta hotuna sannan kuma suka yaɗa su a soshiyal midiya.
“Amma wasu daga cikin waɗanda ba’a san ko su waye ba sun shiga har ɗakin babar ta sun ɗauki hoton ta ana yi mata kwalliya, kuma suka zo suna yaɗawa.”
Ya cigaba da cewa yaɗa irin wannan ba abu bane da ya dace, musamman duba da cewa ita matar ba waje ta fito taje ta yi party ba ko wani abu makamancin haka, a cikin dakin mahaifiyarta aka ɗauki hoton.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com