Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, ta bayyana cewa bata da tabbas ko gwammatin mijinta ta biyawa ‘yan Najeriya bukatun su saboda yawan burikan da suka ci a kan gwamnatin
Aisha Buhari ta bayyana hakan ne cikin wata tattaunawa ta musamman da BBC cikin harshen turanci, inda tace wannan dalilin ne ya sa ta nemi afuwar ‘yan Najeriya.
Ta bayyana dalilin neman afuwar ‘yan Najeriya
A kwanakin baya Aisha Buhari ta ba ‘yan Najeriya hakuri kan wahalhalu da halin matsin rayuwa da suke fama da shi a yayin addu’o’i na musamman da ta shirya a ranar 1 ga watan Oktoba don bikin cika shekara 62 da samun ‘yancin-kan Najeriya.
A kalamanta:
“Burikan da aka ɗora mana suna da matuƙar yawa. Mutane sun ɗora burika a kanmu, kuma wataƙila bayan shekara bakwai ba mu cika musu dukkan wadannan burikan ba.”
“Allah ne kaɗai ya san abin da ke zuciyar mutane. A matsayinka na ɗan Adam, ba ka da hurumin cewa ka yi daidai, ko kuma ka ce ka yi abin da ya kamata. Saboda haka gwamnatin ta yi ƙoƙari, amma ba lallai haka kowa ke gani ba.”
“A wajensu (gwamnatin) sun yi ƙoƙari, Allah kaɗai ya sani. Saboda haka dole mu bai wa ‘yan Najeriya haƙuri ko da mun cika musu burinsu ko ba mu cika ba.” Inji ta
Tana ganin APC za ta yi nasara a zabe mai zuwa
A farkon watan Oktoban ne jam’iyyarsu ta APC mai mulkin ƙasar ta naɗa Aisha Buhari a matsayin jagorar tawagar kamfe ta mata a matakin takarar shugaban ƙasa.
Ko da aka tambaye ta yaya take gani game da yiwuwar samun nasarar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, Aisha Buhari sai ta kada baki tace:
“Me ya sa za ki yi min wannan tambayar? Tsaf kuwa za mu ci gaba. APC ce za ta ci zaɓe. Da izinin Allah.” A cewar ta.
Aisha Buhari ta nemi afuwar ‘yan Najeriya kan matsalar tattalin arziki da ake fama da shi tun shekarar 2015
Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari a ranar Juma’a, 30 ga watan Satumba, ta nemi afuwar ‘yan Najeriya game da matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a fadin kasar tun bayan hawan mijinta kan karagar mulki
Aisha Buhari ta nemi afuwar ne a lokacin da take jawabi a wajen taron sallar Juma’a na musamman da kuma lacca na musamman na ranar samun ‘yancin kai karo na 62.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com