Sheikh Daurawa, fitaccen malamin addinin islama a Najeriya ya yi nasarar yin wuff da zukekiyar budurwa a matsayinsa na Late Comer.
Kamar yadda bayanai su ka nuna, duk da tarin samari na jami’a da wandanda su ka nemi aurenta a hadda kasancewarta mahaddaciya amma malamin ne ya kasance zakara.

An samu rahotan ne a ajin Northern Habiscus inda wata daga ciki ko wani daga ciki ya shaida wa malamar aji ita kuma ta yada har muka samu bayanin.
Sunan budurwar Haulat kuma ta lashe masabakar kasa wacce ake zargin daga nan ne ma malamin ya ganta har yayi sha’awar aurenta.
Nan da nan mutane su ka zabura su na mamakin yadda malamin ya samu nasarar samun damar wannan kyakkyawar budurwa.
Ana sa ran za ayi auren ne a ranar Asabar mai zuwa. Allah ya nuna mana kuma ya sanya alkhairi. Ameen summa Ameen.
Bayan watanni 2, auren jarumar Kannywood da ta zagi Sheikh Daurawa ya mutu
Auren Jaruma Nafisat Ishak, wacce ta fito a shirin Izzar so mai dogon zamani bayan yin aure babu dadewa ya mutu kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta tabbatar.
Sai dai bata shahara ba sai bayan ta yi wata magana ta rashi ladabi ga Sheikh Daurawa, wanda ana tsaka da batun sai aka ji ta yi aure.
Sai dai bayan kasa da watanni biyu da auren kuma sai ga ta an ga ta dawo dandalin TikTok ta ci gaba da raye-rayenta har tana cewa maza ne ba sa iya rike matan shiyasa aure ke mutuwa.
Kuma kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo da ta saki a TikTok, ta ce maza ba sa rike matansu dakyau, ba sa kashe musu kudi kamar yadda su ka saba a waje.
Ta ci gaba da cewa maza su na auren matan da su ka fi karfin ajinsu, tun daga man shafawa, suttura da sauransu, hakan yasa aure yake samun matsala.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com