Fitaccen malamin addinin Muslunci Sheikh Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya buƙaci waɗanda suka ɗora hoton amarya shi ana mata kwalliya a soshiyal midiya da suyi maza su goge shi.
Kwalliya ake mata a ɗakin mahaifiyar ta
Malam Daurawa, a hirar shi da gidan Radiyon Freedom yace kwalliya ake yi mata a cikin ɗakin mahaifiyar ta, amma aka samu wasu a ciki da suka ɗauke ta hotuna sannan kuma suka yaɗa su a soshiyal midiya.
“Amma wasu daga cikin waɗanda ba’a san ko su waye ba sun shiga har ɗakin babar ta sun ɗauki hoton ta ana yi mata kwalliya, kuma suka zo suna yaɗawa.”
Yaɗa irin hotunan fasadi ne
Ya cigaba da cewa yaɗa irin wannan ba abu bane da ya dace, musamman duba da cewa ita matar ba waje ta fito taje ta yi party ba ko wani abu makamancin haka, a cikin dakin mahaifiyarta aka ɗauki hoton.
“To kaga irin wannan duk wanda ya yaɗa ya yaɗa fasadi, yaci amana tunda ba biki akai ba, ba taro akai ba, ba wani guri aka je akai party ba, amma a ɗauko hoton mutum ana yaɗawa.”
Malam Daurawa ya buƙaci duk wanda yasan ya ɗora wannan hoto da ya hanzarta zuwa ya goge shi. Idan kuma mutum bai goge ba, to lallai malamin yace zasu barshi da Allah.
Daurawa yayi Allah ya isa ga waɗanda suka ƙi gogewa
“An sa mata damuwa, tayi kuka, tayi baƙin ciki. Waɗanda sukai wannan sun san sun ɗau alhakinta, wanda duk yasan yasa yaje ya goge, in kuma bai goge ba to zamu masa Allah ya isa.” inji Sheikh Daurawan.
Ita dai wannan amarya ta malam Aminu Daurawa itace Haulatu Aminu Ishaq, gwarzuwar gasar karatun ƙur’ani ta ƙasa baki ɗaya. Itace wacce ta lashe gasar musabaƙar karatun Alkur’ani da aka gudanar ta bana.
Malamin yace wannan ne ya bashi sha’awa kuma ya ke ganin cewa malamai da manyan masu kuɗi ya dace su riƙa rububin auren irin waɗannan mata da Allah ya yiwa baiwar haddace ƙur’ani.
Daurawa ya ƙara da cewa irinsu ne yafi dacewa ace ana nuna darajar su ba wai irin waɗanda suka yi fice a gasar kyau ko kuma wacce tai fice a shafe-shafe ba.
“Ni nasan darajar auren mata masu ilimi. Na aure mata masu ilimi, naga darajar ilimi, naga irin ‘ya ‘yan da suka haifa mun. Shi yasa ni mace da tafi daraja a gurina ita ce wacce take da ilimi.” inji malam Aminu Daurawa.
Za’a dai ɗaura auren idan Allah ya kaimu ranar juma’a mai zuwa a garin Gusau jihar Zamfara.
A wani labarin kuma, anji yadda wani Ango ya fice daga gurin ɗaurin aure bayan gano cewa Amaryar nada yara 4.
A wani ɗan gajeren bidiyo, anga yadda wani ango ya fice daga gurin ɗaurin aure, a yayin da jama’a da dama suka biyo shi suna ta ƙoƙarin bashi haƙuri. Haka nan, an hangi amaryar tana ta sharɓar kuka a yayinda wasu gungun mata ke ƙoƙarin rirriƙeta.
A wani ɗan guntun bidiyo da aka ɗora a Instagram wanda kuma ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani, anga angon ya fito a fusace yana ta kumfar baki, a lokacin da wasu gungun mutane keta ƙoƙarin bashi haƙuri.
Ango ya bayyana cewa amaryar bata taɓa faɗa mishi cewa tana da ‘ya ‘ya ba sai a yanzu da aka zo wajen ɗaurin auren nasu.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com