Fitaccen tauraro a manhajar TikTok, Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya ya yi bayani dalla-dalla dangane da yadda ya samu nasarar siyar da kayan mata ta manhajar.
Yayin zantawarsa da Dala FM a Kano, Idris ya shaida yadda ya fara sana’ar bayan fara tallata wa wasu hajarsu ta magungunan mata, daga nan ya koma sahunsu.
A cewarsa, sanadin TikTok ya samu makudan kudade wadanda duk riba ce ta wannan sana’ar wacce ta karbeshi.
Ya ce ba ya taba damuwa don mutane sun zage shi da kuma wadanda su ke kiransa da dan daudu don a wurinsa hakan nasara ce mai yawa.
Yayin da yayi martani dangane da majar Murja Ibrahim Kunya da mawaki 442 na Safara’u, Mai Wushirya ya ce tafiyarsu ba za ta dade ba.
Ya ci gaba da bayani dangane rayuwarsa ta kasance da kuma sanadin da na fara TikTok.
Jama’a sun sha mamaki bayan matashi bayyana wa ‘yan TikTok ainihin fuskarsa babu ‘filter’
Mutane da dama sun sha mamaki bayan ganin bidiyon wani matashi bayan ya cire filter daga wayarsa. A bidiyon mai ban dariya, an ga yadda wani @roydampz ya bayyana cewa yana so ya nuna wa kowa asalin fuskarsa, Legit.ng ta ruwaito.
Da farko an ga yadda yayi haske ya kuma yi gunin birgewa, daga karshe kuma an ga yadda yayi bakikkirin.
Yanayin sauyawar da kalar fatarsa tayi ya bai wa mutane da dama mamaki, amma mutumin ya yi bayani dalla-dalla.
Ya ja kunnen wadanda su ke mato masa akan su kiyaye, ga asalin yadda halittarsa take.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com