Wata mai bayar da shaida, Hajiya Fatima Ibrahim, ta gayawa wata babbar Kotu a Zaria cewa wadanda suka yi garkuwa da ita sun bata N2000 a matsayin kudin mota bayan sun karbi N6m a matsayin kudin fansa.
Ana musu tuhume-tuhumen da dama ciki har da garkuwa da mutane
‘Yan sanda na karar Dalhatu Shehu, Lawal Aliyu-Bullet, Nuhu Ismaila da Nura Usman da laifukan fashi da makami, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma garkuwa da mutane. Jaridar Daily trust ta rahoto.
Hafsat brahim tana bayar da shaida ne a matsayin shaidar mai kara a zaman da kotun ta dawo don cigaba da sauraron karar a babbar kotu dake Dogarawa, Zaria.
“A ranar 2 ga watan Janairun 2021, cikin dare, na jiyo sautin karar wasu bakin abubuwa. Yayin da na farka na kunna haske, sai nayi arba da wadanda ake karar su hudu dauke da bindiga da adda.”
“Suna son sanin inda mijina yake. Na gaya musu cewa baya nan.”
“Sun sace ni sannan suka tafi dani dajin Galadimawa cikin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, bayan sun dauki kudi, kayan yarana da sauran abubuwa masu amfani daga gidan.”
“Sun kira mijina sannan suka yi cinikin kudin fansa kan N6m wanda za a yi biya biyu.”
“A gabana a ka biya kudin, sannan daya daga cikin su (Usman) ya bani N2000 cikin kudin a matsayin kudin mota,” Ta shaidawa kotu.
Ta bayyana cewa wadanda ake karar sun nuna mata inda zata hau motar da zata kai ta gida sannan suka tabbatar mata cewa ba abinda zai same ta tare da sauran.
Yan sanda sun chafke matar da ta hada baki aka yi garkuwa da mijinta
Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a ta gurfanar da wata mata mai suna Joy Emmanuel ‘yar shekara 40 bisa zargin shirya garkuwa da mijinta, Emmanuel Ebong.
Kwamishinan ‘yan sanda, Olatoye Durosinmi, ya shaida wa manema labarai cewa, Joy da sauran masu garkuwan sun karbi kudi naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa domin a sako mijinta.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com