27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Rikicin Kannywood: Kotu ta bayar da umurnin dole jaruma Hannatu Bashir ta gurfana a gabanta

LabaraiKannywoodRikicin Kannywood: Kotu ta bayar da umurnin dole jaruma Hannatu Bashir ta gurfana a gabanta

Har yanzu dai tsugunne bata kare ba game da rikicin da ya barke tsakanin jarumi Ali Nuhu da jaruma Hannatu Bashir, wacce har ta kai su ga zuwa gaban kotu.

Wata kotun majistiri mai lamba 58, karkashin mai shari’a Aminu Gabari, ta bayar da umurnin cewa dole jaruma kuma furodusa a masana’antar Kannywood, Hannatu Bashir ta gurfana a gaban ta.

Lauyoyi sun bukaci da a basu dama su yi sasanci

Kotun dai ta fara sauraron karar da babban jarumin masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, ya shigar akan jaruma Hannatu Bashir dangane da zargin da yake mata na cin zarafin sa. Kamar yadda majiyar mu ta Dala FM ta rahoto.

Yayin zaman kotun wanda ya gudana a ranar Talata, lauyoyin mai kara da lauyoyin wacce ake kara sun bayyana a gaban kotun, inda suka bukaci kotun da ta amince musu su je suyi sasanci.

Kotun bata amince da bukatar su ba

Sai dai kotun taki amincewa da wannan bukatar ta su inda ta bayar da umurnin dole waccea aka yi kara, wato Hannatu Bashir ta bayyana a gaban Kotu.

Kotun ta sanya ranar 25 ga wannan watan Oktoban da muke ciki, domin ci gaba da gudanar da shari’ar.

Jarumi Ali Nuhu ya yi karar jaruma Hannatu Bashir bisa zargin ta ci zarafinsa, zargin da jarumar ta musanta, inda tace abin da ke tsakanin su shi ne sakon da ta aika masa kan gazawar sa na cika alkawarin zuwa fara daukar film dinta.

Ali Nuhu ya maka jaruma Hannatu Bashir gaban kotu bisa zarginta da cin mutuncinsa

Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya kai karar jaruma kuma furodusa a masana’antar, Hannatu Bashir gaban alkali bayan zarginta da ci masa mutunci ta hanyar tura masa sako kunshe da kalaman cin mutunci.

Salima Muhammad Sabo, lauyar Ali Nuhu ta ofishin lauyoyi na M.L. Ibrahim and Co. ta shigar ga karar ne a kotun majistare da ke lamba 58 a anguwar Nomansland cikin Kano.

Mujallar Fim ta gano yadda Ali Nuhu yayi karata saboda ba a samu abinda ake nema ba a wani fim din Hannatu wanda aka yi alkawari da jarumin kuma ya saba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com


Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe