31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Nayi alƙawarin dorawa daga inda Buhari ya tsaya kan matsalar tsaro – Tinubu

LabaraiNayi alƙawarin dorawa daga inda Buhari ya tsaya kan matsalar tsaro - Tinubu

Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata yayi alƙawarin ɗorawa daga inda gwamantin Buhari ta tsaya kan matsalar tsaro, tattalin arziki da sauransu in aka zaɓe shi a 2023.

Tinubu zai cigaba daga inda Buhari ya tsaya

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake zayyano muhimman abubuwa guda uku da zaiyi in aka zaɓe shi a zaɓen 2023 mai zuwa. Ya shaidawa Buhari cewa zai tafiyar da ayyukan da ya ƙaddamar bayan ya gama a 2023 kamar yadda muka samu daga jaridar Punch.

Yadai gabatar da jawaban ne dai a wajen wani taron kwanaki uku na ministoci da manyan sakatarorin gwamanti da yake gudana a Abuja ranar Talata.

Ya jinjina ma gwamnatin Buhari

Tinubu ya kuma ƙara jinjina ma Buhari bisa ayyukan alkhairin da ya assasa domin cigaban ƙasa. Ya ce Buhari ɗora ƙasar akan turba bayan shekaru da aka ɗauka ana mulkin kama karya.

Tinubu ya ƙara da cewar ba ƙaramar sa’a bace ace ya samu nasarar zama shugaban ƙasar da zai cigaba daga hannun gwamantin da ta yi ayyuka tuƙuru, kuma yayi alƙawarin tabbatar da yayi dora akan ayyukan alkhairan da ake gudanarwa a yanzu.

Tinubu ya bada tabbacin cewa nan gaba idan za’a bada tarihin mulkin Buhari, dole a jinjina mishi bisa ga irin na mijin ƙoƙarin da yayi wajen saka tubalin ginin al’umma da samun zaman lafiya da lumana.

Ya godema Buhari da yawun ‘yan Najeriya

“Saboda haka zai zama abin alfahari a gareni a matsayin ɗan takarar jam’iyyar mu, ace na samu damar bin sawun shugaba Buhari bayan kammala wa’adin shi.”

“Mai girma shugaban ƙasa da sauran muƙarraban sa, ina son shaida muku cewa indai aka zaɓe ni naci, to lallai zan mutunta ayyukan daka bari a baya.”

Tinubu ya jinjina ma gwamnatin ta Buhari kan ƙin watsa ma ‘yan Najeriya ƙasa a ido waɗanda suka yarda dasu suka basu damar jagorantar su.

“Muna godiya mai girma shugaban ƙasa. Ina son na cima ‘yan Najeriya albasa wajen gode maka da kai da muƙarrabanka. Mun goyi bayan ka tun kafin hawanka mulki, kuma zan cigaba da zama aboki kuma amininka har bayan barinka wannan kujerar.

“Ina faɗin hakan ne saboda sanin irin kyawawan ƙudururrukan da kake dasu akan wannan ƙasa, ƙudururruka ne masu kyau sosai. Na san da irin kishin daka mulki wannan ƙasa, haka nan kuma nasan abubuwan daka iya cimma wa.”

A wani labarin na daban kuma, kunji cewa ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa bai aminta da tsarin da aka zo dashi ba wanda wasu ƙungiyoyin ‘yan Arewa suka shirya ga ‘yan takarar dake neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa.

Gamayyar ƙungiyoyi daban-daban na ‘yan Arewa ne dai suka zo da wannan tsari na gayyatar ‘yan takarar shugabancin ƙasa domin gabatar da jawabi.

A wata wasiƙa wacce shugaban yaƙin neman zaɓen na Kwankwaso wato Abdulmumin Jibrin ya aikewa masu shirya taron, ya bayyana musu cewa ya riga da ya tsara cewa zai gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe a wannan ranar da suka sanya.

Sannan Kwankwaso yayi zargin cewa ya samu labarin cewa wasu sun karɓe ragamar gudanarwa tsarin wanda daga ƙarshe suke shirin bayyana goyon bayan su ga wani ɗan takara da sunan Arewa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe