27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Dangin miji sun sabunta lefe tare da hada liyafa ga matar ɗan’uwansu da aurensu ya cika shekaru 10

LabaraiDangin miji sun sabunta lefe tare da hada liyafa ga matar ɗan'uwansu da aurensu ya cika shekaru 10

Wani bidiyo wanda ya dinga yawo a kafafar sada zumuntar zamani ya bayyana yadda dangin mijin wata mata cike fa farinciki yayin da aka nuno wata ta rungumeta. A cikin bidiyon, an ga kayan kwalam da makulashe iri daban-daban tare da akwatuna irin na amare da na yara.

A karkashin bidiyon wanda shafin Arewafamilyweddings na Instagram ya wallafa an bayyana cewa kanwar mijinta ce ta shirya mata liyafar. Sannan ba liyafar kadai bace abin ban sha’awa, ko da gani su na jindadin zama da junayensu hakan yasa su ka rungume juna bayan ganin abubuwan arzikin da aka shirya mata.

Bidiyon ya bayyana yadda matar ta kwashe shekaru 10 da aure inda ta haifi yara, hakan yasa su ka shirya liyafar ta nuna mata kauna. Tabbas bidiyon ya dauki hankali kwarai don kowa ya kalleshi ya san an kashe makudan kudade.

Kuma alamu na nuna tsananin shakuwa da soyayyar da ke tsakanin matar da dangin mijin. Duk da dai babu bayani mai tsawo dangane da bidiyon ko kuma inda aka yi hakan, amma ko da gani mutane ne masu hannu da shuni.

Ga bidiyon:

Tun bayan mahaifiyar mijina ta fado daki ta tarar muna kwanciyar aure da danta ta daina min magana, Matar aure

Wata mata ta koka akan yadda mahaifiyar mijinta ta dena mata magana bayan ta shiga dakin baccinsu ba tare da kwankwasawa ba, ta tarar da ita da mijinta suna tarayya ta auratayya.

Kamar yadda ta bayyana, lamarin ya auku ne bayan surikarta ta kawo musu ziyara na ‘dan wani lokaci, Pulse ta ruwaito.

Tuko.co.ke ta ruwaito yadda matar ta labarta yadda a duk lokacin da mahaifiyar mijinta na nan take kokarin ganin ta janyo rudani tsakaninta da mijinta.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe