Wani dan Najeriya ya shawarci maza akan cewa kada su kuskura su yarda da mata ko kadan bayan ganin yadda soyayyarsa ta kaya da budurwarsa, Legit.ng ta ruwaito.
Sambo Mai Hula ta shafinsa na Twitter na @Abdullahiabba_, ya bayyana yadda abokinsa yaje bikin aminsa a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba inda ya gano cin amanarsa da aka yi.
Ga mamakin abokin Sambo, ashe amaryar mai suna Fatima budurwarsa wacce su ka yi shekaru uku su na soyayya. A cewar Sambo, abokinsa yayi niyyar auren budurwar amma kwatsam ashe mafalkinsa ba zai tabbata ba.
Kamar yadda ya wallafa:
“Kada ka kuskura ka yarda da mace don sai ta ci amanarka. Wannan matashin sun kai shekaru uku su na soyayya da Fatima inda yake da burin aurenta kawai sai yaje bikin abokinsa jiya inda ya gano ashe Fatima ce amaryar. Kada ka kuskura ka amincewa mace.”
Sambo wanda asalin sunansa Abdullahi Abba Sambo ya tabbatar wa Legit.ng gaskiya labarin inda ya bayyana dalla-dalla yadda lamarin ya faru. Dan kasuwar ya bayyana yadda lamarin ya auku a karamar hukumar Ungoggo da ke Jihar Kano.
Bakar hassada ta tunzura matashi halaka abokinsa bayan ganin ya siya dalleliyar mota
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta samu nasarar kama wani mutum bayan ya halaka abokinsa tare da birne gawarsa a gidansa da ke Lokoja, Jihar Kogi.
Bisa ruwayar LIB, lamarin ya auku ne a wuraren Felele da ke Lokoja inda mamacin ke zama da iyalinsa.
An tattaro rahotanni dangane da yadda Kehinde Ajayi, wanda aka halaka, ya samu nasarar siyan mota kirar Toyota Sienna mai kalar ruwan toka a ranar 24 ga watan Yulin 2022.
Sai dai abokinsa yana aikin gyaran na’urar sanyaya wuri ne. Kuma hassada ta sanya shi jan Kehinde zuwa wani wuri da misalin karfe 10 na safiyar ranar da sunan zai taya shi murnar siyan motar.
Majiyoyi sun nuna yadda mutumin ya ja Kehinde da wani zuwa wurin, kuma tun daga nan ba a sake jin duriyarsa ba.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com