31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Abinda muka tattauna da Peter Obi -Sheikh Gumi

LabaraiAbinda muka tattauna da Peter Obi -Sheikh Gumi

Sanannen malamin addinin musuluncin nan Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana abinda suka tattauna da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, a yayin ziyarar da ya kai masa a gidansa dake Kaduna.

Peter Obi ya ziyarci malamin addinin kafin ya wuce wurin taron da wasu gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya suka yi da ‘yan takarar dake neman shugabancin kasar nan.

Ya bayyana muhimman batutuwan da suka tattauna

Da yake magana da jaridar Daily Trust, Sheikh Gumi yace ya tambayi Peter Obi wasu abubuwa duk da cewa wannan ne karon farko da suka taba haduwa a rayuwar su.

“Peter Obi ya kawo min ziyara duk da cewa wannan ne karon farko da muka taba haduwa ido da ido, don haka na yaba sosai da ziyarar da ya kawo min.”

“Nayi masa tambayoyi masu muhimmanci, amma na gaya masa ba sai ya bani amsa nan take ba tunda nasan yana kan hanyar zuwa Arewa House inda zai yi mutane bayani gamsashshe yadda za su gane.”

“Na tambaye shi kan matsayar sa akan yiwa Najeriya garambawul, domin kasar ta samu sauye-sauye tun daga shekarar 1960 har zuwa yau, sannan ta yadda zai zamar da aikin yi a kasar nan.”

“Na kuma tambaye shi yadda zai kwantar da hargitsin da ake a yankunan Kudu maso Gabas, Arewa ta tsakiya, Kudu maso Yamma da Arewa maso Gabas. Sannan na gaya masa akwai ‘yan kasar waje masu kara iza wutar rikici a kasar nan. Ta yaya zai magance hakan?”

“Ya yarda cewa akwai kasashen waje masu tsoma baki kan lamuran kasar nan. Daga nan sai nayi masa fatan alkhairi.” A cewar sa.

Ya shawarci masu neman shugabancin kasar nan

Sheikh Gumi ya kuma shawarci dukkanin ‘yan takarar shugaban kasar da mayar da hankali wajen yakin neman zabe kan abubuwa masu muhimmanci.

Ya kuma gargade su akan yin kalaman da ka iya kara dumama yanayin siyasar da ake ciki a kasar nan.

Nafi Buhari ƙaunar Najeriya nesa ba kusa ba -Sheikh Ahmed Gumi

Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari baya ƙaunar ƙasar nan kamar yadda yake yi.

Sheikh Ahmed Gumi ya faɗi hakan ne yayin da yake martani kan kamun da hukumar DSS tayi wa Tukur Mamu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe