27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

“Aikin yi yayi wuya” budurwa ‘yar Najeriya ta koma bara a kasar waje, ta bishe da neman taimako

Labarai"Aikin yi yayi wuya" budurwa 'yar Najeriya ta koma bara a kasar waje, ta bishe da neman taimako

Wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna Adetemi, ta garzaya manhajar TikTok inda ta nuna irin bakar wahalar da take wurin rayuwa a Birtaniya.

Budurwar ta bayyana cewa ba kowane mutum bane da ya koma kasar waje yake rayuwa mai kyau kamar yadda mutane suke tunani.

Kasar waje ba kamar yadda mutane ke tunani bane

Adetemi, wacce tayi magana cikin harshen Yarbanci, tace ta fita yawon bara ne da fatan kila ta iya haduwa da wani wanda zai iya bata aikin da zata yi. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

A kalamanta:

“Na fara barar neman kudi domin na samu abin sawa a baki. Har yanzu na kasa samun aikin yi…A inda nake bara yanzu, idan da rabo zan iya samun wanda zai sanya na samu aikin yi… Tuni na mika takardu na inda suka dace….”

Ta bayyana cewa babban dalilin da ya sanya tayi bidiyon shine domin ta nuna cewa kasar waje fa ba kamar yadda ake zuzutata bane, inda ta kara da cewa mutane da dama na amsar kebura kamar ta.

Ta bayyana cewa:

“Duk lokacin da na gayawa mutane halin da nake ciki, ba su yarda. Bayan na fito bara nan waje sannan wani ya bani abinci. Da ace na tsaya ciki ban fito ba, da zan samu wannan abincin na kyauta?”

Dalilin zuwan budurwar kasar waje

Adetemi tace mutanen dake wucewa wani lokacin su kan bata kayayyaki kamar kayan sanyawa ko sabulu.

Budurwar ta kuma cigaba da cewa rashin ilmi a kasar waje babbar matsala ce. Ta bayyana cewa neman maganin rashin lafiyar dan ta, ita ce silar zuwanta kasar waje.

Budurwa ta fusata, ta bazama neman saurayin da zata yi wuff da shi, bidiyon ya dauki hankula

A wani labarin na daban Kuma, wata budurwa ta bazama neman saurayin da za ta yi wuff da shi.

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana cewa ta gaji da zama ba saurayi. Budurwar ta garzaya wani babban shago domin nemo saurayi.

Bayan ta isa shagon, budurwar tayi bidiyo inda take bayyana cewa ba taje shagon bane domin siyawa kanta kayayyaki ba.

A cewar ta makasudin zuwanta shagon shine samo saurayi. Ta kara da cewa bata damu ba da duk wanda ta samu ko da kuwa saurayin wata ne daban.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe