Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana cewa ta gaji da zama ba saurayi. Budurwar ta garzaya wani babban shago domin nemo saurayi.
Bayan ta isa shagon, budurwar tayi bidiyo inda take bayyana cewa ba taje shagon bane domin siyawa kanta kayayyaki ba.
A shirye take tayi wuff da saurayin wata
A cewar ta makasudin zuwanta shagon shine samo saurayi. Ta kara da cewa bata damu ba da duk wanda ta samu ko da kuwa saurayin wata ne daban. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
A kalamanta:
“Ku na dai ganin inda nake yanzu ko. Ban zo nan ba domin siyan wani abu. Na zo neman saurayi ne. Zan shiga shagon nan da sunan ubanhiji.”
“Sannan ‘yar’uwa, ki sani cewa idan saurayin ki ya zo wajena shikenan ta faru ta kare. Ya tafi kenan. Da gaske ake hidimar, ba a bori da sanyin jiki. Ba a tsaya wa sanya.”
Ga bidiyon nan kasa:
Mutane sun tofa albarkacin bakin su
Ifeomaonye ta rubuta:
“Wane ‘yar’uwa ta, mazajen arziki na can na aiki a ofisoshin su. ‘Yan Yahoo-yahoo za ki hadu da su a nan.”
Veevogee ya rubuta:
“Wasu na rabuwa, wasu na neman saurayi. Kaga wannan rayuwar.”
Vickyflamez ya rubuta:
“Ki sani cewa cikin sauki za ki iya kwace makashin matar aure a shagon. Mutane yakamata su dinga taka tsan-tsan.”
Ba zan yi aure ba har abada – inji saurayin da budurwa ta ha’inta
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya bayyana irin ha’intar da budurwar sa tayi masa
Wani matashin saurayi mai suna Seyi Oluleye da budurwa shi ta ha’inta ya fito ya shelanta wa duniya cewa shi da aure har abada, ba zai yi ba kwata-kwata.
Saurayin ya bayyana hakan ne a shafin shi na twitter a ranar Juma’ar data gabata, inda ya bayyana cewa ya gano cewa budurwa shi da yake shirin ya aura ta ha’ince shi, ya kamata tayi lalata da wani namiji daban.
“A yau ina son bayyana ma duniya cewa Ni Seyi Oluleye ba zan taɓa yin aure ba har abada. Ba zan taɓa ba. Nasan dangina zasu taru domin tattauna batun nawa, amma ko a jiki na. Bazan taɓa yin aure ba.” inji saurayin.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com