Hukumar ‘yan sandan jihar Abia ta bayyana cewa ta cafke wani jami’in dan sanda bisa bindige abokin aikin sa.
Dan sandan da aka halaka mai suna Samuel Ugor, wanda Insufeta ne, an bindige shi ne bayan gardama ta barke a tsakanin su.
Da yake bayani a wani taron manema labarai, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Godfrey Ogbonna, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin a babban birnin jihar Umuahia.
A cewar jaridar The Cable, ‘yan sandan biyu suna aiki a karkashin Ginger Onwusibe, dan majalisa mai wakiltar mazabar Isiala Ngwato a majalisar dokokin jihar Abia.
Kakakin hukumar ‘yan sandan ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Asabar, inda ya kara da cewa tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin.
Ogbonna ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma abin Allah wadai, inda ya kara da cewa ‘yan sandan daga SPU Base 15, Anambra, suke amma suna aiki a karkashin dan majalisar.
An garkame Dan sandan da yayi harbin
Ya bayyana cewa jami’in dan sandan da yayi yana a garkame yanzu haka, yayin da aka tafi da gawar mamacin a wurin aje gawarwaki.
“Lamarin yana karkashin binciken sashin SCID domin zakulo makasudin aukuwar wannan danyen aikin.” Inji shi
Wani lokacin ‘yan sanda na harbi ba gaira ba dalili
Duk da dai bai cika aukuwa akai-akai ba, akwai lokutan da jami’an ‘yan sanda ke bindige abokan aikin su kan dalilai mabambanta.
A watan Yunin 2021, an cafke wani jami’an dan sanda a Enugu bayan yayi harbi kan mai uwa da wabi wanda yayi sanadiyyar halaka mutum biyar.
Yadda dan sanda ya tasa keyata wurin mai POS, na cire N100,000 ya amshe, Matashi
Wani dan Najeriya ya yi wata wallafa a Twitter wacce ya ke neman a taimaka masa akan wata mugunta da dansanda yayi masa a yankin Aguda da ke Legas, LIB ta ruwaito.
A cewarsa, dan sanda ya dakatar da shi ne, inda ya amshe masa Naira dubu dari take yanke. Mutumin mai amfani da suna @ojogbadura, ya ce jami’an tsaro su na kiransa da dan damfarar yanar gizo saboda yana amfani da na’ura mai kwakwalwa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com