31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Da takalminsa muka gane shi, cewar ɗalibai bayan malaminsu yaje makaranta da Usaininsa

LabaraiDa takalminsa muka gane shi, cewar ɗalibai bayan malaminsu yaje makaranta da Usaininsa

Wani matashi ya wallafa wani bidiyo akan yadda dan uwansa da su ke tagwaye ya kai masa ziyara a makarantar da yake aiki a matsayin malami, Legit.ng ta ruwaito.

Yayin da dan uwansan ya shiga aji, dalibai da dama sun yi mamaki inda su ka dinga kallonsu kasancewar kamar tasu har ta baci.

Yayin da wasu su ke ta wahala wurin bambanta su, nan da nan wasu daliban masu dabara su ka duba kafafunsu inda su ka gane malaminsu da takalminsa.

A wani bidiyo wanda shafin @twindiaries na TikTok su ka wallafa aka ga bidiyon wanda ya dauki hankalin mutane da dama.

Daliban sun yi matukar mamaki kasancewar ba su taba sanin cewa malaminsu tagwaye bane sai a ranar.

Duk da halittarsu iri guda, haka kuma tufafin da ke jikinsu, amma abin ban mamakin shi ne takalminsu ya bambanta wanda hakan yasa su ka yi saurin gane malaminsu.

Bayan fadi darasinsa, dalibai 11 sun daure malamin lissafi jikin bishiya, sun lakada masa dukan tsiya

Rundunar ‘yan sanda ta ruwaito yadda dalibai 11 su ka taru wurin daure malamin lissafinsu jikin bishiya tare da zane masa jikinsa, Nigerian Pulse ta ruwaito.

Sai da su ka ja shi zuwa harabar marakantar da sunan za su tattauna da shi dangane da wata jarabawar da ya basu har su ka fadi.

Daga nan ne su ka kama malamin, Suman Kumar, bayan ya bayyana musu makin da su ka ci a shafin yanar gizon makarantar, Soneram Chaure, sannan su ka daure shi jikin bishiyar tare da zane shi.

Bidiyoyi da hotunan yadda lamarin ya auku sun bazu a shafukan sada zumunta inda kowa yaga yadda aka zane mutumin.

Kamar yadda odditycentral.com ta ruwaito, bincike ya bayyana yadda daliban su ke a fusace inda daya daga cikinsu ya nuna dukan da malamin yayi masa bayan ya fadi darasin har da bandeji a kansa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe