Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya nemi abokin hamayyar sa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar, da ya janye ya mara masa baya a babban zaben shekarar 2023 dake tafe.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 17 ga watan Oktoban 2022, a yayin wani taron tattaunawa da shugabannin yankin Arewacin Najeriya a karkashin inuwar kwamitin hadaka na Arewa a birnin Kaduna. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya nemi Atiku da ya mara masa baya
Da yake bayani akan makasudin yin wannan furucin na sa, Tinubu ya nemi Atiku da ya mayar da halaccin da yayi masa lokacin da nemi takarar shugaban kasa a shekarar 2007 a karkashin tsohuwar jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN), ta hanyar janye kudirin takarar sa ya mara masa baya.
Taron da ake yi da shugabannin yankin Arewacin Najeriya, na daga cikin wata muhimmiyar tattaunawa da ake da wasu zababbun ‘yan takarar shugaban kasa domin tattaunawa da su akan shirye-shiryen da suke da su akan yankin kafin zuwan babban zaben shekarar 2023.
An dai gudanar da taron ne a Arewa House a birnin Kaduna.
Ka taimaka ka goyi bayana domin in cimma nasara – Tinubu ga El-Rufai
A wani labarin na daban kuma, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nemi gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da ya goya masa baya domin samun nasara.
Dan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya roƙi gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai akan ya goyi bayan shi don ganin ya cimma nasara a zaɓen 2023 dake gabatowa.
Tinubu yadai yi wannan roƙon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tattalin arziƙi da kasuwanci da ya gudana ranar Asabar a Kaduna, kamar yadda majiyar mu ta Vanguard ta wallafa.
Da yake jinjina ma gwamnan, Tinubu yace Najeriya na buƙatar shugaba mai kaifin basira irin su Nasiru El-Rufai
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com