Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi ram da wadansu matasa da ake zargin ‘yan DJ ne yayin da su ka dakko kayan kidan DJ dinsu zuwa wurin da ‘yan Takutaha su ke inda dinka dinga kwasar rawar Asosa.
Malam Shehu Tasi’u Ishaq, mukaddashin kwamandan Hisbah na ayyukan yau da kullum ya bayyana yadda aka kama matasan.
A cewarsa, an yi ram da su yayin da aka kama su dumu-dumu da wasu abubuwan da ake zargin ba su yi kama da na Takutahar ba.
A cewarsa, dakarun hukumar fiye da 500 wadanda su ka sanya idanu yayin bikin ne su ka kama su, kuma yanzu haka su na nan tantancesu don daukar matakan da su ka dace akansu.
A tattaunawar da Dala FM tayi da wasu daga cikin masu DJ din sun bayyana cewa sun ji nasihar da aka musu kuma idan shekara ta zagayo za su tabbatar sun koyi wakoki don su bayyana a sha’irai.
Hukumar Hisbah ta ƙona kwalaben giya na maƙudan kuɗaɗe a Jigawa
Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta ƙona kwalaben giya sama da 5,550 wanda darajar kuɗin su takai N3.2m.
Da yake magana bayan kammala aikin a ƙaramar hukumar Kazaure ta jihar, shugaban hukumar na jihar Jigawa, Ibrahim Dahiru, yace kayan mayen an kama su ne a zagayen da hukumar ke gudanarwa yanzu. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
Ya bayyana adadin giyar da aka ƙwato
A cikin sati biyu mun ƙwace giya ta kai kwalabe 5,500 wanda kuɗin su yakai N3.2m. A cewar sa
Dahiru yace an gudanar da aikin ne bayan samun izni daga kotu wanda ya bayar da damar lalata giya.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com