Shugabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Legas, sun bayyana goyon bayan su ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kungiyar na jihar Reverend Stephen Adegbite, shine ya bayyana hakan a ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Za su fuskanci fushin ubangiji idan ba su goyi bayan dan takarar ba
Adegbite yace ubangiji zai hukunta kungiyar addinin idan ta kasa goyon bayan Tinubu a zaben 2023.
A kalaman sa:
“Ubangiji zai hukunta mu idan bamu goyi bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.”
“Na gayawa abokan mu daga Arewacin Najeriya cewa Asiwaju Bola Ahmed, dan takarar mu ne sannan zamu goya masa baya.” Inji shi.
Shugaban ya bayyana wasu ayyukan da dan takarar yayi musu
Shugaban yace ba wanda ya isa ya hana CAN ta jihar Legas daga goyon bayan takarar Tinubu saboda ayyukan arziki da dumbin taimakon da yayi wa Kiristanci a yankin Kudu maso Yamma.
Ya bayyana yadda tsohon gwamnan na jihar Legas, ya fara shirin biyawa Kiristoci zuwa Jerusalem, shirin da har yanzu suke amfani da shi.
“Wannan shekarar ma zamu je kuma za muyi masa addu’a.”
“Kada kuma ku manta Tinubu shine ya dawowa da makarantu hannun mamallakan su lokacin yana gwamma. Akwai abubuwa da dama, don haka zamu goya masa baya.”
Adegbite yayi wadannan kalaman ne a wurin taron da ‘yar majalisar dattawa tayi, Sanata Oluremi Tinubu, Sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya.
Ka taimaka ka goyi bayana domin in cimma nasara – Tinubu ga El-Rufai
A wani labarin na daban kuma, Tinubu ya roki El-Rufa’i da ya goya masa baya don samun nasara a zabe mai zuwa.
Dan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya roƙi gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai akan ya goyi bayan shi don ganin ya cimma nasara a zaɓen 2023 dake gabatowa.
Tinubu yadai yi wannan roƙon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tattalin arziƙi da kasuwanci da ya gudana ranar Asabar a Kaduna
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com