34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Ban aminta da tsarin da aka zo dashi ba – Kwankwaso ga ‘yan Arewa

LabaraiBan aminta da tsarin da aka zo dashi ba - Kwankwaso ga 'yan Arewa

Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa bai aminta da tsarin da aka zo dashi ba wanda wasu ƙungiyoyin ‘yan Arewa suka shirya ga ‘yan takarar dake neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa.

Gamayyar ƙungiyoyi daban-daban na ‘yan Arewa ne dai suka zo da wannan tsari na gayyatar ‘yan takarar shugabancin ƙasa domin gabatar da jawabi, kamar yadda Dailytrust ta wallafa.

Wasu sun karɓe ragamar gudanarwa

A wata wasiƙa wacce shugaban yaƙin neman zaɓen na Kwankwaso wato Abdulmumin Jibrin ya aikewa masu shirya taron, ya bayyana musu cewa ya riga da ya tsara cewa zai gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe a wannan ranar da suka sanya.

Sannan Kwankwaso yayi zargin cewa ya samu labarin cewa wasu sun karɓe ragamar gudanarwa tsarin wanda daga ƙarshe suke shirin bayyana goyon bayan su ga wani ɗan takara da sunan Arewa.

“Mun samu bayanai kan cewa wasu daga cikin mutanen da suka shirya taron an riga da an siye su, kuma sun riga da sun gama shirya wa tsaf don su nuna goyon bayan su ga wani ɗan takara guda ɗaya a yayin taron.

Ana shirin nuna goyon bayan ɗan takara guda ɗaya

“Munyi amannar cewa ba tsari bane ace wasu su shirya maƙarƙashiyar da zasu nuna goyon baya ga ɗan takara guda ɗaya da sunan Arewa, musamman kuma da ya zamto cewa ba ɗan takara ɗaya kadai garemu daga yankin Arewa ba.”

Ya ƙara da cewar ko ranar da aka shirya yin taron da farko saida aka ɗaga ta domin tayi daidai da ranar da wani ɗan takara ya gudanar da yaƙin neman zaɓen shi a Kaduna.

Kwankwaso ya gargaɗi masu shirya taron

“Mun fahimci cewa ranar da aka tsaida da farko sai da aka ɗaga ta domin kawai tayi daidai da ranar da wani ɗan takara ya gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen shi a jihar Kaduna. Wannan shine ya bamu tabbacin cewa wancan ɗan takarar ne ya ɗauki nauyin duka tsarin.” kamar yadda ya bayyana.

Daga ƙarshe, Kwankwaso yayi kira ga mashirya taron akan su guji nuna goyon baya ga wani ɗan takara guda ɗaya domin gudun kada su ƙara rarraba kawunan ‘yan Arewa.

A wani labarin na daban kuma, Dan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya roƙi gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai akan ya goyi bayan shi don ganin ya cimma nasara a zaɓen 2023 dake gabatowa.

Tinubu yadai yi wannan roƙon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tattalin arziƙi da kasuwanci da ya gudana ranar Asabar a Kaduna, kamar yadda majiyar mu ta Vanguard ta wallafa.

Da yake jinjina ma gwamnan, Tinubu yace Najeriya na buƙatar shugaba mai kaifin basira irin su Nasiru El-Rufai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe