Dan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya roƙi gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai akan ya goyi bayan shi don ganin ya cimma nasara a zaɓen 2023 dake gabatowa.
Najeriya na buƙatar irin su El-Rufai
Tinubu yadai yi wannan roƙon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tattalin arziƙi da kasuwanci da ya gudana ranar Asabar a Kaduna, kamar yadda majiyar mu ta Vanguard ta wallafa.
Da yake jinjina ma gwamnan, Tinubu yace Najeriya na buƙatar shugaba mai kaifin basira irin su Nasiru El-Rufai.
“Ina tabbatar maka da cewar zan ci zaɓen nan da goyon bayan ka, kuma na san cewa kai mai goyon bayana ne sosai. Nasan Kaduna kamar gida take a gurina.
Zan maida hankali kan matsalar tsaro
“Zamu cigaba da maida hankali wajen tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a duka yankunan mu. Ina da tabbacin cewa ƙarƙashin shugabanci na zamu maida hankali wajen bin tsare-tsaren yaƙi da ta’addanci na musamman daga jami’an tsaron mu, zamu yi yaƙin tare.” inji Tinubun.
Tinubu ya baiwa El-Rufai tabbacin cewa a ƙarƙashin shugabancin shi bazai zura ido ya bari ‘yan ta’adda da ‘yan fashi su karɓe iko da wani yanki ba.
“Zamu cigaba da bada horo da kuma kayan aiki na zamani ga zaƙaƙuran jami’an tsaron mu domin tabbatar da sun magance matsalolin tsaro a yankunan mu. Najeriya zata cimma nasara da cigaba, ina baka tabbaci. Zan kafa gwamnati mai inganci da zata tabbatar da tsaron kuɗaɗen ƙasa ta hanyar amfani da fasahohin zamani.”
Tinubu ya roƙi El-Rufai da ya tsaya ya taimaka mishi.
“Idan ka barni a kan mimbarin yaƙin neman zaɓe, zan cigaba da yaƙin ne ni kaɗai. Muna buƙatar basirarka da dubararka a zaɓen 2023 mai zuwa.”
A wani labarin kuma, kunji labarin Mutanen dake tono gawarwakin ‘yan uwansu duk bayan shekara 3.
Mutanen ƙabilar Toraja dake da zama a kudancin yankin Sulawesi dake ƙasar Indonesiya na gudanar da bikin tono gawarwakin ‘yan uwansu duk bayan shekara uku kamar yadda al’adar tasu ta tanadar.
A cewar su, wannan al’ada dai da mutanen na Toraja keyi suna yin tane domin su riƙa tsaftace gawarwakin ‘yan uwansu da suka mutu. mutanen sun maida wannan al’ada biki wanda yake gudana a duk bayan shekara uku. Sunyi ma bikin laƙabi da ‘bikin Ma’nene’ ma’ana bikin tsaftace gawarwaki da suka rigaye su.
Yadda suke gudanar da bikin shine, ‘yan uwan mamatan na jini zasu samu majiya ƙarfi sai suje can inda aka bizne matattu, sai su gano ƙabatin ‘yan uwan nasu sannan kuma sai su haƙo su. Daga nan za’a zo da gawarwakin gida, a sake yi musu wanka sannan ayi musu kwalliya iri daban-daban.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com