34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

An samu asarar rai bayan magoya bayan APC da PDP sun ba hammata iska a jihar Zamfara

LabaraiAn samu asarar rai bayan magoya bayan APC da PDP sun ba hammata iska a jihar Zamfara

Hukumar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar da cewa mutum daya ya rasu, yayin da wasu mutum 18 suka samu raunika bayan barkewar wani rikici a tsakanin wasu kungiyoyin matasan APC da PDP a jihar.

A cewar ‘yan sandan, kungiyoyi biyun da suka ba hammata iska dai ana zargin cewa magoya bayan jam’iyyar APC da jam’iyyar PDP ne a jihar. Jaridar The Cable ta rahoto.

An tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Gusau, babban birnin jihar ranar Lahadi.

“An fara gudanar da bincike kan lamarin domin tabbatar cewa wadanda suka aikata wannan danyen aikin sun fuskanci fushin hukuma”.

An yi musayar yawu tsakanin APC da PDP

Jam’iyyar APC ta jihar Zamfara, a ranar Asabar ta bayyana cewa ‘yan daban da ake zargin magoya bayan PDP ne suka kitsa harin.

Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ya fitar na cewa:

“Abin akwai ban takaici hari dauke da makamai da ‘yan daban PDP suka shirya”.

“’Yan daban sun zo ne a matsayin yaran dan takarar gwamnan PDP na Zamfara sannan suka yi harbi akan matasan da ba su ji ba, ba su gani ba wadanda suke aikin su na wata-wata na tsaftace muhalli a unguwar GRA ta Gusau, babban birnin jihar”.

“Muna kira ga mutanen da ‘yan daban suka bata wa rai da su kwantar da hankulan su. Muna kira ga gwamnatin jiha da hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo masu laifin domin hana aukuwar daukar fansa”.

Da take martani akan zargin da ake, jam’iyyar PDP, tace dan takarar ta, Dauda Lawal-Dare, taro kawai yayi domin tarbar wadanda suka sauya sheka daga kananan hukumomi 14 na jihar a ranar Asabar.

A cewar Murkhtar Lugga, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, jam’iyyar ta karbi mutum 50 daga kowace karamar hukuma a jihar.

Sai dai, ya kuma yi zargin cewa an farmaki wasu matasan jam’iyyar PDP a yayin taron, inda ya kara da cewa an harbi biyu daga cikin magoya bayan jam’iyyar a harabar ofishin yakin neman zaben dan takarar gwamnan a Gusau.

Lugga yace jam’iyyar za ta gudanar da bincike kan zargin rikicin da aka yi da wanda ya hada da magoya bayan ta, sannan ta dauki matakin da ya dace.

Gwamnatin Najeriya za ta kawo karshen rashin tsaro nan da watan Disamba – Cewar Aregbesola

Hukumar tsaro ta kasa, NSC, ta bayyana cewa irin yadda hukumomin tsaro ke kokari za ta kawo karshen rashin tsaro nan da watan Disambar wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a yau Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron NSC da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe