Kada ka auri ‘yar talaka, ba ta san soyayya ba, burinta ta kubuta daga talauci, Uba ga dansa. Wani mutum dan Najeriya ya bayyana shawarar da ya bai wa dansa dangane da aure inda yace kada ya kuskura ya auri diyar talakawa, LIB ta ruwaito.
A wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter, mutumin ya ce yana bayyana hakan ne bisa yadda rayuwa ta koya masa hankali, kuma ya dawo ya gane gaskiya.
Ya ce tabbas ‘ya’yan talakawa ba sa yin soyayya tsakani da Allah, don ba su santa ba. Kamar yadda ya wallafa:
“Na shawarci da na jiya akan cewa ya kiyaye soyayya da yaran talakawa. Bisa yadda na kula da soyayya, yawancinsu ba su santa ba kuma ba su yarda da ita ba.
“Burinsu kawai su kubuce daga mawuyacin yanayin da su ka tsinci kawunansu. Sannan su ne masu ceto ‘yan uwansu daga talauci don su fitar dasu daga fatara. Ba sa godiya akan kananun abubuwa, kullum burinsu ka kara kaimi, cewa kana iya yin fiye da haka.”
PDP ba zata taba barin satar dukiyar talakawa ba -Lai Mohammed
Ministan watsa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, yace ba zai taba yiwuwa ba jam’iyyar PDP ta sauya daga dabi’arta ta satar kudaden kasa ba idan har ta sake samun damar komawa kan mulki.
Ministan ya bayyana Hakan ne a yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nigeriya (NAN) a ranar Alhamis a birnin Arusha na kasar Tanzania.
Lai Mohammed na tsokaci ne kan rahotannin da ke cewa wasu daga cikin ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa sun dawo da N122.4 miliyan da shugaban jami’iyyar ya tura musu. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Akwai rahotannin da ke yawo cewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu, ya biya sama da N100 miliyan ga ‘yan kwamitin bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com