34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Matsalar tsaro: An dakatar da wani babban basarake

LabaraiMatsalar tsaro: An dakatar da wani babban basarake

Gwamnatin jihar Enugu ta sanar da dakatar da wani babban basaraken jihar.

Gwamnatin ta dakatar da Greg Ituma, basaraken masarautar Ekpulato Mgbowo, a karamar hukumar Awgu ta jihar. Jaridar The Cable ta rahoto.

An dakatar da basaraken bayan wani taro kan lamuran tsaro

A cikin wata sanarwa da kwamishinan harkokin masarautu na jihar Enugu, Charles Egumgbe, ya fitar ranar Asabar, yace an tsimma matsayar dakatar da basaraken ne bayan gudanar da wani taro kan lamuran tsaro a ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, an dakatar da basaraken ne bisa zarge-zargen da ake masa kan sa hannu cikin lamuran dake barazana ga tsaron jihar.

Zai cigaba da kasancewa a dakace har sai an kammala bincike

Sai dai, sanarwar kuma bata fayyace hakikanin abinda basaraken yayi ba da har aka dakatar da shi.

Egumgbe ya kuma kara da cewa, basaraken zai kasance a dakace har sai zuwa lokacin da gwamnatin jihar ta kammala bincike da neman shawarwari kan lamarin.

Taron na lamarin tsaron da aka gudanar dai ranar Juma’a ya wakana ne a karkashin jagorancin gwamnan jihar, Ifeanyi Uguwanyi.

Sauran mahalarta taron sun hada da, mataimakiyar gwamnan jihar Cecilia Ezeilo, kakakin majalisar dokokin jihar Edward Ubosi; da sakataren gwamnatin jihar Simon Ortuanya.

Wakilan hukumomin tsaro da suka samu halartar taron sun hada da, sojojin kasa, sojojin sama, jami’an NSCDC, ‘yan sanda da kuma ‘yan sandan farin kaya (DSS).

Gwamnatin Najeriya za ta kawo karshen rashin tsaro nan da watan Disamba – Cewar Aregbesola

A wani labarin na daban Kuma, Aregbesola yace gwamnatin Najeriya za ta kawo karshen matsalar tsaro Nan da watan Disamba.

Hukumar tsaro ta kasa, NSC, ta bayyana cewa irin yadda hukumomin tsaro ke kokari za ta kawo karshen rashin tsaro nan da watan Disambar wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a yau Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron NSC da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Mista Aregbesola ya kuma sanar da rusa kwamitin yaki da safarar makamai da alburusai da kuma lalata bututun mai, NATFORCE.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe