27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Mutanen dake tono gawarwakin ‘yan uwansu duk bayan shekara 3 (hotuna)

LabaraiLabaran DuniyaMutanen dake tono gawarwakin 'yan uwansu duk bayan shekara 3 (hotuna)

Mutanen ƙabilar Toraja dake da zama a kudancin yankin Sulawesi dake ƙasar Indonesiya na gudanar da bikin tono gawarwakin ‘yan uwansu duk bayan shekara uku kamar yadda al’adar tasu ta tanadar.

Ana tono gawarwakin don a tsaftace su

A cewar su, wannan al’ada dai da mutanen na Toraja keyi suna yin tane domin su riƙa tsaftace gawarwakin ‘yan uwansu da suka mutu. mutanen sun maida wannan al’ada biki wanda yake gudana a duk bayan shekara uku.  Sunyi ma bikin laƙabi da ‘bikin Ma’nene’ ma’ana bikin tsaftace gawarwaki da suka rigaye su, kamar yadda muka samu daga Guardian.

99b5dfd09e3c4a2c82dbc89cfc6ba6d7

Yadda suke gudanar da bikin shine, ‘yan uwan mamatan na jini zasu samu majiya ƙarfi sai suje can inda aka bizne matattu, sai su gano ƙabatin ‘yan uwan nasu sannan kuma sai su haƙo su. Daga nan za’a zo da gawarwakin gida, a sake yi musu wanka sannan ayi musu kwalliya iri daban-daban.

Ana barin gawarwakin waɗanda basu daɗe da mutuwa ba a gida har ya zuwa lokacin da za’a yi musu bikin biznewa na musamman. Mutanen kan tara kuɗaɗe domin ganin sunyi ma ‘yan uwansu biznewa ta musamman.

tarojan dead person 2

Yadda abun ya samo asali

Wannan al’ada da dai ta tono gawarwaki daga makwancin su ta daɗe ana gudanar da ita, shekaru aru-aru. Ance ta samo asali ne daga wani mafarauci da yayi kaciɓus da wata gawa a yayin da yake yawon farauta a yankin Torajawan. Mafaraucin sai ya dauki gawar, ya tsaftace ta, ya sanya mata tufafin shi, wanda a cewar mutanen hakan ya kawo mishi sa’ar rayuwa.

Tun daga wannan lokaci sai abun ya zama bikin al’ada wanda ake gudanarwa har ya zuwa yanzu. Sai dai kuma a wani ƙaulin, ance mutanen suna yin hakan ne domin ƙara samun kusanci ga mamatan.

8fc5316e55904283ae231c04110173f2 2

Ana yima gawarwakin ado iri-iri

A yayin bikin, ana yima gawarwakin mamatan da aka tono ado, a sanya musu sababbin kaya. Haka nan ana canja musu akwatunan da suke ciki a sanya su cikin sababbi. Sannan kuma ana kewayawa da su cikin unguwannin da akan san sun taɓa zuwa a lokacin rayuwar su.

Wannan ƙabila dai ta mutanen Toraja dake tono gawarwaki na da mutanen da yawansu ya kai aƙalla mutane 450,000 waɗanda mafiya yawa daga cikinsu Kiristoci ne. Haka nan a cikin su akwai Musulmai, sannan kuma akwai ‘yan addinin gargajiya.

A wani labarin kuma, wani saurayi yace ba zai yi aure ba har abada saboda budurwar shi ta ha’ince shi.

Wani matashin saurayi da budurwa shi ta ha’inta ya fito ya shelanta wa duniya cewa shi da aure har abada, ba zai yi ba kwata-kwata.

Saurayin ya bayyana hakan ne a shafin shi na twitter a ranar Juma’ar data gabata, inda ya bayyana cewa ya gano cewa budurwa shi da yake shirin ya aura ta ha’ince shi, ya kamata tayi lalata da wani namiji daban.

“A yau ina son bayyana ma duniya cewa Ni Seyi Oluleye ba zan taɓa yin aure ba har abada. Ba zan taɓa ba. Nasan dangina zasu taru domin tattauna batun nawa, amma ko a jiki na. Bazan taɓa yin aure ba.” inji saurayin.

Yin wannan rubutu na shi keda wuya a shafin nashi na tuwita ne dai ya fara karɓar saƙuna da yawa daga ‘yan mata daban-daban, waɗanda yace sun rinƙa tambayar shi akan ko yana da muradin ya aure su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe