27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Ina tausaya ma shugaban ƙasar da zai hau nan gaba – Sanusi Lamiɗo

LabaraiIna tausaya ma shugaban ƙasar da zai hau nan gaba - Sanusi Lamiɗo

Tsohon sarkin Kano mai martaba Sanusi Lamiɗo sunusi ya bayyana cewa yana matuƙar tausaya ma shugaban ƙasar da zai gaji kujerar shugabancin ƙasa bayan Buhari ya kammala wa’adin shi, saboda halin taɓarɓarewar tattalin arziki da ƙasar ke ciki.

Sanusi yayi jawabin ne a wajen taron tattalin arziki

Sanusi dai ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a yayin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taron tattalin arziki da jihar Kaduna ta shirya a garin Kaduna kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.

Khalifan tijjaniya kuma tsohon sarkin Kano, sanusi ya ƙara da cewa Najeriya ta ta’allaƙan kacokan akan mai da kuma iskar gas wajen samun kuɗin shiga, kuma da zarar an cire kuɗaɗen tallafin man sai kaga abubuwa suna yin baya..

Najeriya ta ta’allaƙa akan bashi

Sanusi ya kuma bayyana cewa Najeriya dai na cigaba da kasancewa a ƙasa mai dogaro da cin bashi. Sai dai ba’a amfani da bashin yadda ya kamata, illa iyaka wasu ne ke handame kuɗaɗen domin suyi ta ƙara azurta kawunan su.

“In anyi zaɓen 2023, ba zamu iya cigaba da tafiya akan wannan tsarin ba. Saboda in aka cigaba da tafiya a haka to lallai zamu faɗa mummunan matsalar rashin tsaro irin na Mali ko Burkina Faso.

“Ba zamu cigaba da tafiya a kan haka ba, dole ne mu dawo mu sake tsari.” inji Sanusi.

Kaso 50 na jihohi basa iya riƙe kansu

Da yake cigaba da jawabin, Sanusi ya bayyana cewa aƙalla kaso hamsin na jihohin da suke a Najeriya basa iya samar da wadatattun kuɗaɗen da zasu iya yin albashi da kuma gudanar da sauran abubuwa irin su biyan bashi da sauran su.

Ya ƙara da cewa kuɗaɗen da Najeriya ke buƙata wajen rage bashi sun wuce abinda ƙasar ke samu. Yace tana buƙatar naira tiriliyon 2.597 domin rage bashi, a yayin da ita kuma ƙasar iya naira tiriliyon 2.4 take iya samu.

“A taƙaice dai, kuɗaɗen rage bashi sun kai kaso 108 na abinda ƙasar ke iya samu. Kunga kenan duk wata naira ɗaya da gwamnatin tarayya ta samu tana ƙarewa ne wajen rage bashi, kuma ba isa zata yi ba, tunda dole sai gwamanti ta ranto wasu kuɗin don rage bashin. Sannan sai gwamanti ta ƙara ranto kuɗi sannan take iya gina hanyoyi da sauran ayyuka.

“Muna ta ƙara jibgar bashi mai tarin yawa ga ‘ya ‘yanmu. Can gaba ƙila sai sun tsine mana saboda duk mun kwashe kuɗaɗen da muka ranto wajen biyan tallafin mai don mu siye shi a arha.

“Muna ganin matsala, kuma muna cigaba da tafiya a haka. Ina tausaya ma shugaban ƙasar da zai karɓi karagar mulki a watan Yunin baɗi, kuma yazo yace yana don cire tallafin mai bayan karɓar mulkin.” inji Sanusi Lamiɗo

A wani labarin, kunji cewa gwamnatin Zamfara ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga a wasu ƙananan hukumomi.

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da dokar taƙaita zirga-zirga a wasu ƙananan hukumomi bisa dalilin ta’azzarar matsalar tsaro data addabesu.

Ƙananan hukumomin da abun ya shafa sune Gummi, Anka da kuma ƙaramar hukumar Bukkuyum. Dokar dai ta hau kan garuruwan Yarkofoji, Birnin Tudu, Rini, Gora Namaye, Janbako, Faru, Kaya, Boko da kuma Mada. Hakan ya biyo bayan ƙaruwar yawaitar ayyukan masu garkuwa da mutane da kuma sauran nau’o’in ta’addanci.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Ibrahim Dosara ne dai ya fitar da sanarwar ga manema labarai a ranar juma’a da ta gabata.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe